![]() |
Bahaushe a ranar Bikin Hawan Sallah |
Kamar yadda Wazirin Kano Alhaji Abubakar Dokaji ya kawo a littafin mai suna "Kano Ta Dabo Ci Gari" ya bayyana cewa idan ana son yin magana akan Tarihin Hausawa ko Kasar Hausa dole sai an leka cikin tarihin Sudan. Shi kuma tarihin Sudan sai an leka cikin tarihin daular Larabawa ta Banu Umayyah da Banu Abbasiyyah. Haka kuma da bincike akan labarin yadda wasu Jama'a suka dinga yin kaura daga tsakiyar nahiyar Asiya suka taho yamma. Don haka tarihin Hausawa yana da alaka da wannan yankuna da muka ambata.
Ita kasar Sudan wani yanki ne a nahiyar Africa wanda daga gabas tayi iyaka da kasar Habasha (Ethiopia a yanzu), daga Arewa tayi iyaka da Sahara, daga kudu tayi iyaka da yankin sunkurun kurmin nan na tsakiyar Africa wato African Rain Forest a turance. Kalmar nan 'Sudan' tana nufin 'baki' saboda galibin al'ummar dake zaune a cikin yankin Sudan bakaken fata ne. A wannan zamanin yankin Sudan ya hada kasashe kamar Jamhuriyar Sudan, Chad, Arewacin Cameroon, Arewacin Nigeria, Niger, Arewacin Benin, Arewacin Togo, Arewacin Ghana, Burkina Faso, Mali, Arewacin Cote d'Ivoire, Guinea, Guinea Bissau, Gambia, da kuma Senegal.
Yankin Kasar Hausa yana cikin yankin da ake kira "Sudan Ta Tsakiya" wato "Central Sudan a Turance. Daga gabas tayi iyaka da Kasar Borno, daga yamma tayi iyaka da Kasar Dahomey (wadda yanzu ake kira Jamhuriyar Benin), daga Arewa tayi iyaka da Hamadar Sahara, daga kudu kuma tayi iyaka da Kasashen Nupe wanda ake Kira "Middle Belt".
Masana tarihi da yawa sun tabbatar da cewa Hausawa sun samo asali ne daga yankin gabas musamman kasar Habasha ko yankin Larabawa. Mulkin Banu Umayyah da na Abbasiyyah a yankin Larabawa ya saka Mutane da yawa sun yi kaura daga nan zuwa yamma har zuwa yankin kasar Hausa. Misali, ya tabbata cewa akwai kamanceceniya ta harshe tsakanin Hausawa da kasar Habasha. Ita kanta sunan Hausa yayi kama da sunan Habasha. Ga wasu misalin kalmomi:
(1) Habashawa - Hausawa
(2) Damina - Damina
(3) Zug Zug - Zuga Zugi
An ce wadannan mutane da suka yi kaura daga Habasha sun zauna a yankin Kasar Daura da kuma kasar Kano. Misali a Kano akwai Dutsen Dala wanda aka ce mazauna Dutsen Mafarauta ne wanda suka taso daga yankin Dahalak dake kasar Habasha. Don haka ne suka sakawa Dutsen suna Dala daga Dahalak.
Kammalawa (Conclusion)
A takaice dai Hausawa da asalin su ya tabbawa cewa daga yankin gabas ne. Wannan shine abin mafi yawancin Masana Tarihi suka tabbatar.
0 Comments