Sarkin Kano Bagauda ya kasance daya daga cikin yayan Bawo Sarkin Daura. Kuma shi Bagauda an ce ya kasance cikakken mayaki wanda ya kware a wajen yaki da kuma iya mulkin jama'a. Wannan yada daya daga cikin manyan dalilai da suka bashi damar kafa Masarautar Kano a shekarar 999 A.D., kuma ya samar da nagartaccen mulki wanda ya zama tushen Masarautar Kano.
Kamar yadda Kundin Tarihin Kano na "Kano Chronicle" ya bayyana, ance lokacin da Bagauda yazo Kano sai ya iske wasu daga cikin ragowar fadawan Barbushe irin su Jankare masu bautar Tsumburbura. Da farko Bagauda bai ci nasarar mallakar jama'ar da ya tarar a Kano yadda ya kamata ba. Daya daga cikin manyan Kano a wannan lokaci wanda ake kira Jankare bai amince da zuwan Bagauda ba. Don haka ne aka gwabza yaki tsakanin mayakan Bagauda da jama'ar Jankare. Bagauda yayi nasara har ma ya kama Jankare tare da yanka shi. Daga nan Bagauda ya iske alkaryun Gazargawa wadanda ke zaune daga Jakara zuwa Damargu, da alkaryun Zadawa wadanda ke zaune daga Santolo zuwa Barkum, da alkaryun Zaura wanda suke zaune a Bompai zuwa Wasai, da alkaryun Dundunzuru dake daga Watari zuwa Dutsen Karya, alkaryun Sheme dake Damargu zuwa Kazaure, da Gande dake Barkum zuwa Kera, da alkaryun Tokarawa dake daga Karmami zuwa Ringim. Mazawada shine wanda Bagauda ya samu babba cikin wadannan mutane dake zaune a Kasar Kano.
Bagauda yazo sai ya sauka a Dinari ya shekara biyu sa'annan ya koma Burka ya gina Talotawa, daga nan ya koma Sheme. A can ya iske wadansu manyan matsafa wadanda ya mallake su, sune Galosami, Barmi, Gazawari, Dabgege, Fasa-Taro da Bakin Bunu.
Tarihin Kano ya tabbatar da cewa Bagauda bai sami rinjaye akan mutanen Kano dukan su ba har ya mutu bayan ya shekara sittin yana kokarin tabbatar da ikon sa a matsayin Sarkin Kano.
Kamar yadda muka fada a tarihin Kafuwar Birinin Kano a baya, mun fada cewa Bagauda yana da Fadawa ko Hakimai wanda suka taimaka masa wajen gudanar da mulki. Wadannan Hakimai sune kamar haka:
- Kududdufi (wanda sarautar sa daga baya ta zama Dan Kududdufi)
- Buram (Dan Buram)
- Isa (Dan Isa)
- Akasan (Dan Akasan)
- Darman (Dan Darman)
- Goriba (Dan Goriba)
0 Comments