TARIHIN SARKIN KANO ALU MAI SANGO

 

Hoton Sarkin Kano Alu Mai Sango

Sarkin Kano Alu wanda ake yiwa lakabi da "Mai Sango" ya kasance dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo Basullube. Mahaifiyar sa ita ce Saudatu yar Sarkin Musulmi Alu Babba. Yayi Mulkin Kano daga shekarar 1894 zuwa 1903.

Alu Mai Sango ya zama Sarkin Kano bayan da Yakin Basasar Kano ya kare, wanda yayi sanadiyyar tunbuke Sarkin Kano Muhammadu Tukur daga karagar Sarautar Kano. Tarihi ya tabbatar cewa bisa umarnin wan sa wato Galadiman Kano Yusufu cewar inda an samu nasarar tunbuke Sarkin Kano Tukur daga karagar mulki, to a nada Alu. Don haka bayan Yakin Basasar, sai mafi yawancin manyan Gidajen Fulani a Kano suka yi masa mubayi'a. Da hawan sa karagar mulki, Sarkin Kano Alu ya himmatu wajen sake fasalin gudanar da Masarautar Kano. Misali, duk Dagatai a kasar Kano wanda suka goyi bayan Sarkin Kano Tukur to an cire su tare da maye gurbin su da magoya bayan Yusufawa. Haka kuma ya nada wasu manyan Hakimai domin su taimaka masa wajen gudanar da mulki kamar haka :

  1. Waziri: An nada Ahmadu dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi
  2. Galadima: An nada Shehu dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi
  3. Madaki: An nada Kwairanga dan Madakin Kano Umaru Nayaya
  4. Ciroma: An nada Mamuda dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi
  5. Dan Iya: An nada Malam Gajere dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi
  6. Ma'aji: An nada Umaru
  7. Magajin Malam: An nada Musa dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi
  8. Santuraki: An nada Muhammadu Nakande dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi
  9. Sarkin Dawakin Tsakar Gida: An nada Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi
  10. Sarkin Gaya: An nada Jarmai Dila


Yake-Yaken Sarkin Kano Alu Mai Sango

Mafi yawancin masana tarihin Kano sun tabbatar da cewa Sarkin Kano Alu Mai Sango ya kasance cikakken mayaki wanda baya tsoron yaki. Don haka ne Masarautar Kano ta sha fama da yake-yake daga waje. Misali, Kanawa sun sha fafatwa da Masarautar Damagaram ta kasar Jamhuriyar Nijar a yau. Sarkin Damagaram Amadu Kuren Daga ya taba kawo harin yaki a shekarar 1896 inda Sarkin Damagaram din da kan sa ya jagoranci yakin. Sarkin Kano Alu ya fito, kuma an gwabza yaki a Gezawa. An ce wani mayakin Sarkin Damagaram mai suna Mayana yayi wa Sarkin Damagaram alkawarin zai kama Alu, sai ya doso inda Alu yake akan doki, sai bayin Sarkin Kano suka yi kan Mayana, sai Sarkin Kano Alu yace su bar shi ya karaso. Yana isowa kan Sarki Alu, sai Alu ya zare takobi yayi masa tsagar rama wato ya raba shi biyu. Da labari yaje kunnen Sarkin Damagaram Amadu, sai yace "Lallai babu wanda zai iya yiwa Mayana haka sai Sarkin Kano da kan sa. Daga Sarkin Kano Alu ya zaburi dokin sa yayi kan Damagarawa da sara wanda daga karshe mayakan Kano suka raraki Mayakan Damagaram har iyakar Kano da Daura. A wannan yaki Sarkin Kano Alu shigar buzaye yayi watakila saboda ya saje da rundunar Sarkin Damagaram wadda take cike da buzaye. An ce wata zabiyar Sarkin Damagaram ta dinga waka tana cewa:
"Akwai wani buzu cikin Kano, Da an sami bakwai ya shi, Da ba mu kai Damagaram ba"


Turawa sun Cinye Kano

A zamanin Sarkin Kano Alu Mai Sango ne Turawan Ingila suka mamaye Kano tare da kafa mulkin Mallaka a shekarar 1903. Amma kafin Turawa su ci Kano da Yaki, tuni Sarkin Kano bisa rashin sani ya tafi Sokoto domin kai ziyara ga sabon Sarkin Musulmi wato Sarkin Musulmi Attahiru II. An ce lokacin da Sarkin Kano ya yace zai yi tafiyar, Madakin Kano Kwairanga ya bashi shawara akan Kada yayi tafiyar saboda an samu labarin Turawa sun tunkaro Kano, amma dai Sarki ya tsananta akan sai yayi tafiyar. Daga nan Sarki Alu yasa aka tara masa dukkan Hakiman sa da Dagatai, da wasu muuhimman mutane na kasar Kano don tafiya Sokoto. Jama'ar sa Sarki ya tafi da su Sokoto na kan Dawaki da masu tafiya a kasa sun fi mutum dubu goma. Kafin ya tafi kuma yasa aka tara masa manyan malamai domin suyi addu'a don kada Nasara wato Turawa su zo garin Kano. Ashe kaddara ta riga fata, Turawa ma suna gab da isowa Kano. Sarkin Kano Alu ya isa Sokoto a wajejen hantsi inda ya fara ziyara.

Bayan Sarki ya gama ziyarar sa a Sokoto, sai ya baro garin Sokoton ya nufo Kano. Suna kan hanyar dawo wa wani yaron Sarkin Shanun Kano yazo ya bawa Sarkin Kano Alu labarin cewa bayan tafiyar sa zuwa Sokoto Turawa sun ci Kano da yaki, sun kashe Sarkin Shanun Kano Dangwari a gidan Sarki, sun kuma kashe babban Dagacin Sarki wato Sarkin Bebeji Jibir. Da jin wannan shawara, sai Sarkin Kano tare da wasu yan tawagar sa suka tafi birnin Goga inda suka yi alkawari da Sarkin Musulmi za su hadu domin tafiya neman taimako akan Turawa ba tare da kowa ya sani ba. Akan hanya Sarkin Kano Alu ya yi zango a birnin Kwanni. To a birnin Kwanni ne Magajin Garin Kwanni ya aikawa turawan Faransa cewa maza-maza su zo ga Sarkin Kano Alu a kasar sa. Ba tare da sanin Sarki ba, tuni Turawa sun iso masaukin sa inda suka kama shi, kuma suka dauki hoton sa kofar masaukin sa kusa da wani babban daki.

Sarkin Kano Alu
Sarkin Kano Alu da hadiman sa a Lokoja 

Daga birnin Kwanni Turawan Faransa suka damka Sarkin Kano a hannun Turawan Ingila. Su kuma Turawan Ingila suka dauke shi zuwa Yola ta kasar Adamawa. Daga bisani suka canza masa mazauni zuwa Lokoja. A Lokoja ya zauna tare da wasu Sarkuna wanda Turawa suka tube daga Sarauta irin su Sarkin Bida Abubakar, Sarkin Musulmi Tambari, da Sarkin Zazzau Alu dan Sidi. A cikin shekarar 1926 Allah ya yiwa Sarkin Kano Alu Mai Sango rasuwa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu