Yakin Basasar Kano ya kasance wani yaki tsakanin yayan Sarautar Kano akan rigimar sarautar Kano wanda ya afku daga shekarar 1893 zuwa shekarar 1894. Wannan rigima an yi ta ne tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Tukur da magoya bayan sa da ake kira"Tukurawa", da kuma Galadiman Kano Yusufu da Magoya bayan sa wanda ake kira"Yusufawa". Wannan rigima ta janyo yaki wanda ya raba gidan Sarautar Kano, da ma kasar Kano gida biyu. An yi yakin na tsawon shekara daya, kuma daga karshe Yusufawa sun samu nasarar tunbuke Sarkin Kano Muhammadu Tukur daga kan karagar Sarautar Kano.
Dalilin Yakin Basasa
An ce lokacin da Sarkin Kano Muhammadu Bello ya rasu, mafi yawancin Kanawa sun fi son a nada Galadiman Kano Yusufu babban dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi. An ce shi Yusufu ya kasance kasaitaccen basarake wanda Kanawa suke kauna. Kuma mafi yawancin Kanawa a birni da kauye suke fatan ya zama Sarki bayan rasuwar kanin mahaifin sa wato Sarkin Kano Bello. Sai dai kash, lokacin da Sarkin Kano Muhammadu Bello ya rasu, sai Sarkin Musulmi Abdurrahman ya bayar da umarnin a nada Muhammadu Tukur babban dan Sarkin Kano Muhammadu Bello a matsayin sabon Sarkin Kano. Wannan dalilin ya janyo tawaye daga bangaren Yusufu da magoya bayan sa. Kuma hakan ya janyo rabuwar kai a fadin kasar Kano. Har ta kai Dagatai a fadin kasar Kano sun rabu gida biyu. Da masu goyon bayan Sabon Sarkin Kano wato Tukur, da kuma masu goyon bayan Galadiman Kano Yusufu. Daga karshe dai ta tabbata sai an gwabza yaki a Kano.
Galadima Yusufu da mayakan sa suka fita daga cikin birnin Kano tare da yin sansani a Takai domin su hada karfin su guri guda. A takai ne Yusufawa suka hada rundunar yaki mai karfi.
Afkuwar Yakin Basasa
Daga Takai Mayakan Tawaye na Yusufawa suka yi sansani a Garko, daga Garko suka iso Dawakin Kudu. Daga Dawaki Mayakan Tawaye na Yusufawa suka nufo birnin Kano, kuma suka hadu da mayakan Sarkin Kano a Tudun Maliki. Aka gwabza yaki, yan tawaye suka rinjayi Mayakan Sarkin Kano Tukur. Don haka dole tasa Sarki Tukur ya bar garin ya nufi Yamma domin guduwa Sokoto neman mafaka. Sai mayakan Yusufawa suka bi shi inda suka same shi a Tafashiya ta kasar Katsina. A nan aka gwabza karamin yaki, kuma Sarkin Kano Muhammadu Tukur ya hadu da ajalin sa. Don haka karshen mulkin Tukur yazo a shekarar 1894 bayan Shekara daya kan mulki.
Domin Karin Bayani ku latsa bidiyon dake kasa:
Tushen Bayani (References):
Abubakar Dokaji (1958), Kano Ta Dabo Ci Gari, Gaskiya Tafi Kwabo Cooperation, Zaria.
0 Comments