TARIHIN SARKIN KANO MUHAMMADU BELLO

Sarkin Kano Muhammadu Bello ya kasance dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Shima Sarkin Kano Bello mai Babban Daki Shekara ce ta haife shi. Wato kenan sun fito ciki daya da Sarkin Kano Usman Maje Ringim, da kuma Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi. 

Bayan da Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ya rasu a cikin shekarar 1882, sai Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin a nada Turakin Kano Muhammadu Bello a matsayin sabon Sarkin Kano. A lokacin da aka nada Muhammadu Bello ya riga ya manyanta, don haka yana tarin gogewa akan makamar mulki da iya hulda da jama'a.

A zamanin mulkin Sarkin Kano Muhammadu Bello rigingimu na yan uwan taka da na waje sun dabaibaye mulkin sa. Sarki Bello sai da ta kai ya raba gari da yayan dan uwan sa Abdullahi Maje Karofi, wanda suke da yawa sosai, wannan kuma ya janyo rabuwar kai a tsakanin yayan sarautar Kano. Haka wasu daga cikin manyan dagatai a kasar Kano sun yi wa Sarki tawaye. Misali, dubi tawayen da Sarkin Kila Amadu yayi wa Kano. Haka kuma Kano ta sha fama da hare-haren yaki da mayakan Maradi wanda har sai da Sarkin Kano Bello ya nada daya daga cikin sarakunan yakin sa wanda ake kira da Danwaire. An ce Danwaire ya aike wa Jarman Maradi wai shi Danbaba yace su gamu a Ruma ta kasar Katsina. Da suka gamu sai aka ja daga, aka bar wa Danwaire da Danbaba fagen yaki. Suka fara gwabza yaki, bayan wani lokaci Danwaire ya sari Danbaba da takobi har ya mutu. Shikenan yaki ya mutu, gayyar mayakan Maradi suka watse, daga fitinar Maradawa ta kare har abada.

Sarkin Kano Muhammadu Bello ya rasu a shekarar 1893 bayan ya shafe kusan Shekara goma sha daya yana mulki. An nada shi Sarkin Kano a shekarar 1882, ya rasu a shekarar 1893. 

Post a Comment

0 Comments

Close Menu