TARIHIN SARKIN KANO ABDULLAHI MAJE KAROFI

 


Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ya kasance dan Sarkin Kano Ibrahim. Shima mai Babban Daki Shekara ce ta haife shi, kuma an saka masa sunan Abdullahi ne saboda Malam Abdullahi Danfodio wato Abdullahin Gwandu kanin Shehu Usman Danfodio.

Tarihi ya tabbatar da cewa Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi mutum ne dogo, mai kwarjini, mutum mai himma, mai cika alkawari, kuma jarumin gaske. Yayi Mulkin Kano daga shekarar 1855 zuwa shekarar 1882, wato dai ya shekara goma sha bakwi yana sarautar Kano. A zamanin mulkin sa sarautar Kano kara samun ingantuwa tare da samun daukaka. Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi wanda ake yiwa lakabi da "Abdullahi Mai Kano" ya tsayar da mulki mai karfi irin na mahaifin sa Sarkin Kano Dabo. Shi kuma dai ake yi masa kirari da cewa "Abdullahi dagi maganin kasa mai tsauri".

Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi idan ya hau karagar mulki zai fara Shari'a yakan daga yatsar sa sama yace "Wallahi tallahi zan taka shi ko da dana ne, dukkan wanda na samu ya taka Shari'a". A lokacin mulkin sa, Sarki Abdullahi ya zartar da hukuncin kisasi da kuma haddi wato wanda yayi kisa da ganganci a kashe shi. Kuma an yiwa barayi hukunci daidai da su inda rike yanke hannun barayi kamar yadda Allah Madaukaki yayi umarni.

A bangaren kula da kuma tafiyar da ulkin kasar Kano, Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi bai zauna guri daya ba. A tsawon mulkin sa, ya san cikin kasar sa ciki da bai. Misali, taka yakan tashi daga wannan gari zuwa wancan gari domin yin rangadi.

A bangaren tafiyar da arzikin kasa kuma, Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ne ya fara Hukumar Zakka wanda take kula da karbar zakka da rarraba ta ga wadanda suka dace. Haka kuma ya kafa Baitul Mal wato asusun ajiyar hukuma don yin ayyukan kasa da taimakon marasa karfi da gajiyayyu. An samu ci gaba sosai ta fannin kasuwanci a zamanin sa. Baki yan kasuwa musamman daga yankin Arewacin Africa sun shigo Kano sosai domin kasuwanci.

Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ya rasu a cikin shekarar 1882 a yayin da zai tafi Sokoto domin yayi ziyarar ban girma ga Sarkin Musulmi. Ya rasu ne garin Karofi ta Kasar Katsina, wannan dalili ne yasa ake yi masa lakabi da sunan "Maje Karofi".


Tushen Bayani (References)


Abubakar Dokaji, (1958), "Kano Ta Dabo Ci Gari", Gaskiya Tafi Kwabo Printing Press, Zaria.

Abdullahi Nasidi Umaru, 2008, "Daular Fulani a Kano ", Benchmark Publishers, Kano.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu