Sarkin Kano Muhammadu Tukur ya kasance dan Sarkin Kano Muhammadu Bello, dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. An ce a lokacin da Sarkin Kano Bello ya rasu, Wazirin Sokoto yana nan yazo Kano ziyara. Don haka ance tun wannan lokaci Waziri yayi wa babban dan Sarkin Kano Bello wato Galadiman Kano Muhammadu Tukur alkawari cewa shi zai gaji mahaifin sa. Kuma hakan ce ta tabbata, Sarkin Musulmi Abdurrahman yayi umarni a nada Galadiman Kano Muhammadu Tukur a matsayin sabon Sarkin Kano a shekarar 1893. Sai dai kuma mafi yawancin yayan sarautar Kano musamman yayan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi sun ki amincewa da nadin Muhammadu Tukur a matsayin sabon Sarkin Kano. Dalilin kuwa shine cewa babban yayan su kuma babban dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi wato Galadiman Kano Yusuf mai murabus shine yafi cancanta ya zama Sarki. Wannan dalili yasa suka yiwa nadin Tukur tawaye, hakan kuma ya janyo yakin Basasa a Kano daga shekarar 1893 zuwa 1894.
Yazo a tarihi cewa dalilin da yasa Sarkin Musulmi Abdurrahman ya bada umarni a nada Muhammadu Tukur a matsayin sabon Sarkin Kano shine cewa ya taba ceton rayuwar Sarkin Musulmin a wani yaki tsakanin Sokoto da Argungu. An ce lokacin yaki yake shirin afkuwa tsakanin Sokoto da Argungu, sai Sarkin Musulmi ya bukaci Masarautun da suke karkashin Daular Sokoto akan su kawo taimakon yaki. Saboda haka shi Muhammadu Tukur shine ya jagoranci rundunar mayakan Kano domin kai wa Sokoto agaji a rigimar ta da Argungu. A wannan yaki na Sokoto da Argungu, an tabbatar da cewa kwazon da Tukur ya nuna da iya jan daga a fagen fama suka hana Argungu tayi nasara a kan Sokoto. Wannan dalili ne yasa Sarkin Musulmi Abdurrahman ya sakawa Tukur ya nada shi Sarkin Kano.
Yakin Basasa
Kamar yadda muka yi bayani a sama, bayan rasuwar Sarkin Kano Muhammadu Bello mafi yawancin Kanawa sun yi imanin cewa za'a nada Yusufu babban dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi a matsayin Sarkin Kano. Sai dai kash, hakan bata samu ba.
Wannan dukunkune da aka yi na nada Tukur ba tare da masoya da yawa ba, yasa Yusufu da mabiyan sa suka yi tawaye inda suka kafa nasu mulkin a wasu sassan kasar Kano. Haka kuma Yusufu yayi sansani a Takai, kuma daga nan yayi shiri da mayakan sa domin yakar Sarkin Kano Muhammadu Tukur. Sai dai kash ana wannan shiri ne Allah yayi wa Yusufu rasuwa, don haka aka nada kanin sa wato Aliyu wanda ake yi masa lakabi da suna "Alu" akan ya ci gaba da jagorancin yakin. Dalilin nada Alu ya jagoranci yakin shine cewa shi Yusufu yayi wasiyya a nada shi ne saboda shi jikan gidan sarautar Sokoto ne domin kuwa mahaifiyar sa Saudatu yar Sarkin Musulmi Alu Babba ce. Dalilin yin haka kuwa shine saboda da sun kwace Sarauta daga hannun Sarkin Kano Tukur, to Sokoto zata ji kunyar yakar Kano saboda jikan su ne ya karbi mulki.
Daga Takai Mayakan Tawaye na Yusufawa suka yi sansani a Garko, daga Garko suka iso Dawakin Kudu. Daga Dawaki Mayakan Tawaye na Yusufawa suka nufo birnin Kano, kuma suka hadu da mayakan Sarkin Kano a Tudun Maliki. Aka gwabza yaki, yan tawaye suka rinjayi Mayakan Sarkin Kano Tukur. Don haka dole tasa Sarki Tukur ya bar garin ya nufi Yamma domin guduwa Sokoto neman mafaka. Sai mayakan Yusufawa suka bi shi inda suka same shi a Tafashiya ta kasar Katsina. A nan aka gwabza karamin yaki, kuma Sarkin Kano Muhammadu Tukur ya hadu da ajalin sa. Don haka karshen mulkin Tukur yazo a shekarar 1894 bayan Shekara daya kan mulki.
0 Comments