Sarkin Kano Abbas wanda ake yi wa lakabi da "Maje Nasarawa" ya kasance dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Sarki Abbas mutum ne mai rangwame, mai adalci, kuma masoyin jama'a. Ya kasance Sarki wanda ya fara yin zamani da Turawan Mulkin Mallakar Ingila.
A cikin watan Afrilu 1903, Turawa suka tabbatar da Abbas a matsayin Sarkin Kano, kuma lokacin yana rike da sarautar Wamban Kano. Shi ya gaji Sarkin Kano Alu wanda Turawa suka kama suka tafi da shi Lokoja.
![]() |
Sarkin Kano Abbas a lokacin da Turawa suke nada shi |
Sarkin Kano Abbas ya sha wahala a farkon mulkin sa. Wato dai ya samu rashin fahimtar juna da gwamnatin Turawa. An ce dalili na farko shine Turawa sun soke tsarin Jakadu a harkar karbar Haraji, kuma sun maye gurbin su da sabon tsari na Gunduma wato a turance "District Head System". A wannan tsari na Gunduma, Turawa sun raba Masarautar Kano zuwa kasashen Hakimai Ashirin da Hudu. Kuma sun nada Hakimi a kowacce Gunduma. Wannan sabon tsari bai yiwa Sarkin Kano Abbas dadi ba, saboda yana kallon hakan a matsayin wani yunkuri na rage masa karfin iko. Dalili na biyu kuma shine cewa Turawa sun dauko daya daga cikin manyan bayin Sarki wato Danrimi Ala-bar-Sarki suka nada shi Wazirin Kano sarauta ta biyu Masarauta. Wannan ma ya janyo matsala, har an ce shi Ala-bar-Sarki yana hada munafurci tsakanin Turawa da Sarki Abbas. Burin sa idan Turawa suka fusata su cire Sarki su nada shi. Hakan ce kuwa ta kusa faruwa, ba don taimakon Allah ba. Daga karshe dai aka samu sabon Gwamnan Mulkin Mallaka a Kano mai suna C.L. Temple wanda ya kawo masalaha aka samu daidaito da Sarki. Kuma Temple ya bayar da umarnin cire Waziri Ala-bar-Sarki tare da bawa Sarki Abbas wuka da nama akan ya nada sabon Wazirin Kano. Shi kuma Sarki sai ya dauko Muhammadu Gidado ya nada shi matsayin Waziri.
![]() |
Sarkin Kano Abbas tare da wasu daga cikin Hakiman sa a shekarar 1912 |
Tarihi ya tabbatar da cewa Sarkin Kano Abbas mutum ne wanda ya kware a sha'anin mulkin Jama'a, mutum mai kaifin hankali da hangen nesa. Wannan ne dalilin da yasa ya iya tsallake duk wani makircin Turawa.
A lokacin Sarkin Kano Abbas ne aka fara samun ci gaban zamani a Kano. Ga wasu daga cikin abubuwan ci gaban:
1. A zamanin Sarkin Kano Abbas aka gina makarantar boko ta farko a shekarar 1909.
2. A zamanin Sarkin Kano Abbas Jirgin kasa ya fara zuwa Kano a shekarar 1911
3. A zamanin sa aka kafa Baitul Mal tazamani wato asusun ajiyar hukuma. Kuma da shi aka yi amfani aka fara biyan albashin Sarki da Hakimai
4. Turawa suka fara harkokin cinikin gyda wanda ya bunkasa tattalin arzikin Kano.
Rasuwar Sarkin Kano Abbas
Sarkin Kano Abbas ya rasu a shekarar 1919 a gidan Sarkin Kano na Nasarawa, kuma a gidan aka binne shi. Ya shekara goma sha shida yana mulkin Masarautar Kano.
Tushen Bayani (References)
Abubakar Dokaji, (1958), Kano Ta Dabo Ci Gari, Gaskiya Tafi Kwabo Cooperation, Zaria.
Abdullahi Nasidi Umaru, (2008, Daular Fulani a Kano
0 Comments