Sarkin Kano Usman wanda ake yiwa lakabi da "Dan Tsoho" ya kasance dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Yayi sarautar Kano daga shekarar 1919 zuwa shekarar 1926.
An nada Usman ya zama Sarkin Kano bayan rasuwar kanin sa Sarkin Kano Abbas a shekarar 1919. A zamanin Sarkin Kano Usman Dan Tsoho Kano ta samu abubuwan ci gaba musamman ta fannin zamani, domin kuwa a wannan lokaci turawa suna ta yin kokarin tabbatar da kafuwar mulkin mallaka. Ga wasu daga cikin manyan abubuwan ci gaba da aka samu a lokacin:
- An kafa manyan kamfanonin kasuwanci da kantuna kamar su Kamfanin Neja da UAC, da CFAO, da Gidan Goldie da, da GBO.
- An gina dakunan shan magani da asibitoci kamar Shahuci wanda daga baya ya zama Asibitin birnin wato Asibitin Murtala.
- Shigowar abubuwan zamani da Turawan Mulkin Mallaka suka kawo kamar motoci, da kekuna. A wannan lokaci ne ma Turawa suka ba Sarki kyautar mota.
- Gina Gadar Wudil wadda aka gayyaci dan Sarkin Ingila wato Prince Edward yazo ya bude ta. Kuma a wannan lokaci Sarkin Musulmi da sauran Sarakunan Arewa duk sun halarci taron. Wannan gada ita ce ta hada Kano da kasashen Borno da Chadi da sauran kasashen gabashin Africa.
- A lokacin Sarkin Kano Usman Dan Tsoho ne jirgin sama ya fara sauka a Kano. Kuma a wannan lokaci ne jirgi ya fara sauka a tarihin Nigeria.
- Mashahuran yan kasuwar Kano sun fara bayyana irin su Alhaji Alhassan Dantata, Alhaji Nabegu, Alhaji Nagoda, da Alhaji Danbaffa, da sauran su.
Sarkin Kano Usman Dan Tsoho tare da Dan Sarkin Ingila Prince Edward a shekarar 1925 |
Allah yayi wa Sarkin Kano Usman rasuwa a ranar 23 ga watan Mayu, na shekarar 1926.
0 Comments