Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya kasance babban dan Sarkin Kano Abbas, dan Sarkin Abdullahi Maje Karofi, dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Shi Sarki Abdullahi Bayero ya kasance mutum ne mai cika ido, mai kwarjini, mai cika guri. Bayan rasuwar Sarkin Kano Usman Dan Tsoho, sai masu zaben Sarki a Kano suka hadu suka zabi Abdullahi Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano a ranar 15 ga watan Mayu, na shekarar 1926. A lokacin kuwa shi Abdullahi Bayero yana rike da sarautar Ciroman Kano, Hakimin Bichi.
Ci Gaban Kano a Zamanin Sarkin Bayero
Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya kasance Sarki mai hakuri da dattako, da kuma himma wajen gudanar da mulki. Ya kasance basarake mai tafiya daidai da zamani. Wannan dalilin ne yasa Kano ta samu bunkasa sosai a zamanin sa. A cikin shekaru ashirin da bakwai da yayi yana sarauta, Kano ta ci gaba kwarai da gaske cikin kowanne fannin sarauta, ciniki, ilmi, da siyasa.
A harkar mulki abin da Sarki Abdullahi Bayero ya fara yi shine fadada Majalisar Gaban Sarki wacce ke taro duk Laraba ko Alhamis tare da Rasdan (Gwamnan Kano na Mulin Mallaka). A wannan lokaci Sarki da Waziri ne kawai yan Majalisar, amma sakamakon gyaran an shigar da Galadima domin ya kula da sha'anin cikin birni.
Sauran abubuwan ci gaban zamani da aka samu a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero suna hada da:
1. A lokacin sa ne aka fara yiwa gidaje lamba a Kano domin sanin adadin su
2. A lokacin sa ne aka shigo da wutar lantarki, da kuma ruwan sha zuwa cikin birnin Kano.
3. A lokacin sa ne aka gina Makarantar Midil wato Makarantar Rumfa a yanzu.
4. A lokacin sa ne Kofar Kudu da ofishin cikin birni (wato gida mai agogo)
5. A lokacin sa ne aka sake ginin Masallacin cikin gari wanda har ginin haka yake
6. A lokacin Sarkin Kano Abdullahi Bayero ne aka gina Asibitin cikin birni wato Asibitin Murtala a yanzu.
7. A lokacin Sarkin Kano Abdullahi Bayero ne aka fara samun bayyanar malamai masu karancin shekaru irin su Malam Shehu Alhaji Tijjani 'Yan Awaki ', Malam Adamu Na Ma'aji, Malam Nasiru Kabara, Malam Shehu Mai Hula, da sauran su.
8. Kuma Sarkin Kano Abdullahi Bayero ne Sarki na farko da ya fara zuwa aikin Hajji. Yaje Hajjin cikin shekarar 1937.
Rasuwar Sarkin Kano Abdullahi Bayero
Bayan ya shafe shekaru ashirin da bakwai yana sarautar Kano (1926-1953), Allah yayi wa Sarkin Kano Abdullahi Bayero rasuwa a ranar 23 ga watan Disamba na shekarar 1953. Ya rasu yana da shekaru saba'in da takwas a duniya. Bayan an gama an binne shi a Makabartar Gidan Sarki dake Nasarawa, sai masu zaben Sarkin Kano suka zabi babban dan sa wato Ciroman Kano Muhammadu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Kano.
0 Comments