TARIHIN SARKIN KANO MUHAMMADU SANUSI I

Hoton Sarkin Kano Alhaji Sir Muhammadu Sanusi I


Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ya kasance babban dan Sarkin Kano Abdullahi Bayero, dan Sarkin Kano Abbas, dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Yayi Sarkin Kano daga shekarar 1953 zuwa 1963. Kuma ya taba rike Mukaddashin Gwamnan Arewacin Najeriya a shekarar 1957. 

Sarkin Kano Sanusi ya kasance basarake mai Æ™arfin iko da tasiri sosai a Arewacin Najeriya a lokacin mulkin mallaka. Ya shirya babban bikin durbar don girmama Sarauniya Elizabeth II lokacin da ta ziyarci Kano a shekarar 1956. Rikicin mulki tsakanin sa da É—an uwansa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, tare da zarge-zargen almubazzaranci, ya kai ga saukarsa daga mulki, sannan ya tafi gudun hijira zuwa Azare a shekarar 1963. 


Nadin Sanusi a Matsayin Sarkin Kano

An nada Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano a watan Disamba na shekarar 1953, kuma aka bashi sandar Sarauta a farkon shekarar 1954. Ya gaji mahaifin sa Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero.

Hoton Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a lokacin da aka nada shi


Sarkin Kano Alhaji Sir Muhammadu Sanusi ya kasance mutum mai kwarjini da karfin iko wanda Kanawa suke tsoron sa. Farkon abin da ya fara a cikin mulkin sa shine fadada Majalisar Sarki lokacin da ya jawo masu karancin shekaru cikin harkokin mulki. Sarkin Kano Sanusi ya shahara sosai a Nigeria da sauran sassan duniya. Mutum ne wanda bai yarda da raini ba. Ya kasance mai kyautar kasaita don haka bayin Sarki da Malamai suka ji dadin mulkin sa. Shi ya sake karfafa sarautun manyan bayi, ya dawo da nadin su bayan wasu shekaru da Turawa suka hana nada su. A wannan lokacin ya nada Shamaki, Dan Rimi, da kuma Sallama.

Haka kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya kasance mutum mai ilmin Addinin Musulunci. Sarki Sanusi masanin Fikihu ne da Hadisan Manzon Allah (SAW). Sannan kuma ya nakalci hanyoyin Sufaye da Sufanci sosai. Don haka shi ke yin limanci a Masallacin Juma'a har idan yana huduba ba wuya yayi kuka saboda tsoron Allah. A zamanin sa bai bar ashararai sun sake ba. Shi ya hana barayi sakewa, ya rage bala'in karuwanci da sauran dangin barna. 


Zuwan Sarauniyar Ingila 

A shekarar 1956 Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu ta ziyarci Kano har ta shiga cikin gidan Sarki ta sadu da iyalin Sarki, tare da ganin sassan gidan Sarautar Kano. A wannan lokacin an shirya mata Hawan Dawakai na musamman domin a nuna mata yadda al'adar mutanen Kano take. 

Zuwan Sarauniyar Ingila Kano
Sarkin Kano Sanusi tare da Sarauniyar Ingila 


Siyasa da Gwagwarmayar Neman Yancin Nigeria 

Zamanin Mulkin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I yazo daidai lokacin da siyasa take bunkasa tare da gwagwarmayar neman yancin Nigeria. A wannan lokacin Sarkin Kano Sanusi yayi kokari wajen ganin an samu zaman lafiya a tsakanin yan siyasar farko musamman na Jam'iyyun N.P.C da kuma NEPU. 

Haka kuma Sarkin Kano Sanusi yana daya daga cikin manyan kasar nan wanda suka jagoranci samun yancin Nigeria. Ya kasance daya daga cikin manyan Sarakunan Nigeria wanda suka yi amfani da inuwar Majalisar Sarakunan Nigeria wajen ganin Kasar Ingila ta bawa Nigeria yanci. Ya halarci tarukan tattaunawa a gida Nigeria da kuma a birnin London. Daga karshe an samu nasarar samun yancin Nigeria a shekarar 1960.

Sarkin Kano Sir Muhammadu Sanusi
Sarkin Kano Sanusi tare da Turawan Mulkin Mallaka 


Murabus din Sarki Sanusi

Sarkin Kano Alhaji Sir Muhammadu Sanusi I ya bar sarautar Kano a shekarar 1963. An ce dalilin yin murabus din sa shine cewa sun samu sabani da rashin jituwa tsakanin sa da babban aminin sa Firimiyan Jihar Arewa Alhaji Sir Ahmadu Bello. An ce Gwamnatin Jihar Arewa karkashin Sir Ahmadu Bello ta bukaci Sarkin Kano Sanusi ya sauka daga sarauta. Don haka Sarki yayi murabus, kuma ya koma Azare zaman hijra. A zaman sa na Azare ya koma ga harkokin Addini sosai har aka bashin Khalifan Tijjaniyya na Nigeria baki daya. 

Daga baya Gwamnatin Jihar Kano ta Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ta dawo da shi Wudil inda ya zauna a gidan Sarkin Kano dake Wudil, kuma anan ya rasu a shekarar 1991.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu