Sarkin Kano Inuwa. Source: creativecommons.org |
Sarkin Kano Muhammadu Inuwa ya kasance dan Sarkin Kano Abbas, dan Sarkin Abdullahi Maje Karofi, dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Yayi sarautar Kano daga watan Afrilu zuwa watan Oktoba na shekarar 1963.
Rayuwar sa Kafin Zama Sarki
Inuwa an haife shi a kusan shekara ta 1904, daga cikin iyalin Muhammad Abbass, wanda a lokacin shi ne Sarkin Kano. Mahaifinsa ya rasu lokacin yana da shekaru goma sha biyar, sai aka mika shi ga kulawar dan'uwansa Abdullahi Bayero. Lokacin da Bayero ya zama Sarkin Kano a shekarar 1926, ya nada Inuwa Turakin Kano kuma ya sanya shi a matsayin Hakimin Ungogo. A shekara ta 1932, ya zama Hakimin Minjibir. A shekara ta 1939, ya gaji dan'uwansa Abdulkadir dan Abbas a matsayin Galadima Kano kuma aka nada shi Hakimin Dawakin Kudu. Inuwa ya samu tasiri daga malamin Tijaniyya, Shaykh Yahya b. Muhammad Naffakh, kuma an dauke shi a matsayin mai addini da hakuri tsakanin abokansa. A shekarar 1944, ya zama dan Majalisar Masarautar Kano wato Councillor Kano Native Authority kuma daga shekara ta 1952 zuwa 1963, ya kasance memba na Majalisar Wakilai ta Arewa (Northern Regional Assembly).
Inuwa Ya Zama Sarkin Kano
An tabbatar da Muhammadu Inuwa a matsayin Sarkin Kano bayan da Sarkin Kano Alhaji Sir Muhammadu Sanusi I yayi murabus a watan Afrilu na shekarar 1963. A lokacin da aka nada shi Sarkin Kano yana rike da sarautar Galadiman Kano Hakimin Dawakin Kudu.
Sarkin Kano Inuwa ya kasance mutum adali mai sanyin hali da nagarta. Yana da yawan kyauta da sadaka musamman ga malamai da almajirai. A lokacin da yake Sarkin Kano, Sarki Inuwa ya nada wadannan mutane a wasu mukaman sarauta kamar haka:
- Galadiman Kano Ibrahim Ci Gari
- Dan Iyan Kano Abbas Sanusi
- Barden Kano Ci Gari Bayero
- Dandarman Kano Aliyu
- Dokajin Kano Sule Ahmad
- Marafan Kano Sule Minjibir
- Ma'ajin Kano Ali Rano
0 Comments