Gidan Sarautar Kano, da kuma Tambarin Masarautar Kano |
A tsawon shekaru dubu daya da ashirin da hudu wanda Masarautar Kano ta kafu daga Shekarar 999 A.D. har zuwa shekarar 2024 an yi Sarakuna a Kano guda hamsin da takwas. A tarihin Kano an raba wadannan Sarakuna zuwa gidajen Sarauta guda biyu kamar haka:
- Gidan Bagauda
- Gidan Dabo
Wadannan gidajen Sarauta da a turance ake kira da "Dynasty" yana nufin tsatson jini wanda kowanne Sarki ya fito daga ciki. Don haka zamu duba wadannan Sarakunan ta hanyar bin salsalar gidan da suka fito. Sai dai kuma akwai Sarkin Kano Sulaimanu wanda ya kasance ya fito daga tsatson gidan Sarauta daban daga wadannan gidaje guda biyu.
Gidan Bagauda
1. Sarkin Kano Bagauda dan Bawo (999-1063)
2. Sarkin Kano Warisi dan Bagauda (1063-1095)
3. Sarki Kano Gijimasu dan Warisi (1095-1133)
4. Sarakunan Kano Nuta da Magawata yan biyu ne, sun yi mulki tare daga (1133-1135)
5. Sarkin Kano Tsaraki dan Gijimasu (1135-1193)
7 . Sarkin Kano Naguji dan Tsaraki (1193-1247)
8 . Sarkin Kano Guguwa dan Gijimasu (1247-1290)
9 . Sarkin Kano Shekarau I (1290-1307)
10. Sarkin Kano Tsamiya dan Shekarau (1307-1343)
11. Sarkin Kano Usmanu Zamna-Gawa dan Shekarau (1343-1349)
12. Sarkin Kano Aliyu Yaji dan Tsamiya (1349-1385)
13. Sarkin Muhammadu Bugaji dan Tsamiya (1385-1390)
14. Sarkin Kano Kanejeji dan Aliyu Yaji (1390-1410)
15. Sarkin Kano Umaru dan Kanajeji (1410-1421)
16. Sarkin Kano Dauda Bakin Damisa dan Kanajeji (1421 -1438)
17. Sarkin Kano Abdullahi Burja dan Kanajeji (1438-1452)
18. Sarkin Kano Dakauta dan Abdullahi Burja (1452 (Kwana daya yayi)
19. Sarkin Kano Atuma dan Dakauta (1452-1452)
20. Sarkin Kano Yakubu dan Abdullahi Burja (1452 -1463)
21. Sarkin Kano Muhammad Rumfa dan Yakubu (1463-1499)
22. Sarkin Kano Abdullahi dan Muhammad Rumfa (1499-1509)
23. Sarkin Kano Muhammad Kisoki dan Abdullahi (1509-1565)
24. Sarkin Kano Yakubu dan Muhammad Kisoki (1565 -1565)
25. Sarkin Kano Dauda Abasama dan Yakubu (1565-1565)
26. Sarkin Kano Abubakar Kado dan Muhammad Rumfa (1565-1573)
27. Sarkin Kano Muhammad Shashere (1573-1582)
28. Sarkin Kano Muhammad Zaki dan Muhammad Kisoki (1582-1618)
29. Sarkin Kano Muhammad Nazaki dan Muhammad Zaki (1618-1623)
30. Sarkin Kano Muhammad Kutumbi dan Muhammad Nazaki (1623-1648)
31. Sarkin Kano Alhaji dan Muhammad Kutumbi (1648-1649)
32. Sarkin Kano Shekkarau II dan Alhaji (1649-1651)
33. Sarkin Kano Muhammad Kukuna dan Alhaji (1651-1652)
34. Sarkin Kano Soyaki dan Shekarau (1652-1652). (ya sake dawo wa Sarauta) (1652-1660)
35. Sarkin Kano Bawa dan Muhammad Kukuna (1660 1670)
36. Sarkin Kano Dadi dan Bawa (1670-1703)
37. Sarkin Kano Muhammad Sharefa dan Dadi (1703-1731)
38. Sarkin Kano Kumbari dan Sharefa (1731-1743)
39. Sarkin Kano Alhaji Kabe dan Kumbari (1743-1753)
40. Sarkin Kano Yaji II dan Dadi (1753-1768)
41. Sarki Kano Babba Zaki dan Yaji II (1768-1776)
42. Sarkin Kano Dauda Abasama II dan Yaji II (1776-1781)
43. Muhammad Alwali II dan Yaji II (1781-1805)
Jihadin Fulani
44. Sarkin Kano Sulaimanu dan Abuhama (1807-1819)
Gidan Dabo
45. Sarkin Kano Ibrahim Dabo dan Mahmud (1819-1846)
46. Sarkin Kano Usman Maje-Ringim dan Ibrahim Dabo (1846-1855)
47. Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Ibrahim Dabo (1855-1882)
48. Sarkin Kano Muhammad Bello dan Ibrahim Dabo (1882-1893)
49. Sarkin Kano Muhammad Tukur dan Muhammad Bello (1893-1894)
50. Sarkin Kano Alu Mai Sango dan Abdullahi Maje-Karofi (1894-1903)
51. Sarkin Kano Abbas dan Abdullahi Maje-Karofi (1903-1919)
52. Sarkin Kano Usman II dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi (1919-1926)
53. Sarkin Kano Abdullahi Bayero dan Abbas (1926-1953)
54. Sarkin Kano Muhammad Sanusi I dan Abdullahi Bayero (1953-1963)
55. Sarkin Kano Muhammad Inuwa dan Abbas (1963-1963)
56. Sarkin Kano Ado dan Abdullahi Bayero (1963-2014)
57. Sarkin Kano Muhammad Sanusi II dan Ciroman Kano Aminu, dan Sarkin Kano Muhammad Sanusi I (2014-2020). An sake dawo dashi a matsayin Sarkin Kano a shekarar 2024.
58. Sarkin Kano Aminu dan Ado Bayero (2020-2024)
0 Comments