Sarkin Kano Gijimasu dan Warisi ya kasance Sarkin na uku a Jerin Sarakunan Kano. Yayi mulkin Kano na tsawon shekaru arba'in daga shekarar 1095 zuwa 1135.
Tarihin Kano bazai manta da shi domin ya bayar da gudunmawar da baza'a manta dashi ba. Kamar yadda littafin Kundin Tarihin Kano na "Kano Chronicle" ta tabbatar cewa: Sarki Gijimasu ne ya dawo da Mazaunin Masarautar Kano daga Sheme zuwa cikin birnin Kano.
Bayan da Gijimasu ya kafa fadar sa a cikin Kano, sai ya himmatu wajen bawa garin kariya ta hanyar fara ginin ganuwa. An fara ginin ganuwar Kano daga Rariya (tsakanin Kofar Dan Agundi da Kofar Na'isa) yayi yamma zuwa Kofar Adama har zuwa Kofar Tuji babu su yanzu. Wannan aiki da Sarki Gijimasu yayi wa Kano ya bayar da kariya ga birnin, kuma yasa Kano ta kere sa'a a cikin biranen kasar Hausa baki daya.
Ganuwar birnin Kano |
0 Comments