TARIHIN SARKIN KANO MUHAMMADU RUMFA (1463-1499)

Zanen hoton Sarki Rumfa

Sarkin Kano Muhammadu Rumfa dan Sarkin Kano Yakubu ya kasance mafi shahara da tasiri a jerin Sarakunan da suka mulki Masarautar Kano. Yayi mulkin Kano daga shekarar 1463 zuwa 1499. 

Kamar yadda Kundin Tarihin Kano mafi dadewa wato "Kano Chronicle" ya fada : Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya kasance mutum mai ilmi wanda yake tsayawa akan maganar sa. Babu wani Sarki da ya ciyar da Kano gaba fiye da shi. Kano ta samu ci gaba ta fannin ci gaban kasuwanci, shugabanci, da kuma addinin Musulunci.

Bunkasar Masarautar Kano 

Babban abin da Sarkin Kano Muhammadu Rumfa yayi domin karfafa ikon Masarautar Kano shine gina gidan Sarkin Kano wanda har yanzu yana nan, kuma har yau ana kiran Gidan Sarautar Kano da suna "Gidan Rumfa". Kafin wannan lokaci, Sarakunan Kano ba'a nan suke da mazaunin mulkin su ba. 

Fadar Masarautar Kano (Gidan Rumfa)

Haka kuma Sarkin Kano Rumfa ne ya fito da wasu al'adun Sarautar Kano wanda ya banbantata da sauran Masarautun Kasar Hausa. Wadannan al'adu sune kamar haka:

  1. Sarki Rumfa ne ya fara yin bikin Hawan Sallah duk fadin kasar Hausa 
  2. Sarki Rumfa ne ya fito da al'adar rike Tagwayen Masu lokacin da ya dauki masun Sarakunan Kano yan biyu Wato Nuta Magawata ya hada su ya dinke. Har yanzu Sarakunan Kano suna rike Tagwayen Masu
  3. Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya fara fito al'adar Kakaki da Figini da Takalmin gashin jimina 
  4. Sarki Rumfa ne ya kirkiro tsarin Dawakin Zage a lokacin da yake yaki da Katsina saboda canjin doki idan wani ya kasa. 

Ci Gaban Musulunci 

A zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, addinin Musulunci ya samu tagomashi da ci gaba sosai har takai birnin Kano ya zama cibiyar ilmi. Kano ta sake wayewa sosai daga duhun jahilci. A zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa manyan Malaman addinin Musulunci sun zo Kano tare da yada addinin ga mutane. Wasu daga cikin manyan Malaman sune Sheikh Abdul-Karim Al-Maghili da kuma Sheikh Imam al-Suyudi.

Lokacin da Sheikh Abdul-Karim Al-Maghili yazo Kano, ya samu karbuwa a gurin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa har ta kai Sarki ya bashi gurbi a cikin fadar Masarautar Kano. Don haka ne Sheikh Al-Maghili ya umarci Sarki Rumfa ya gina masallacin Jama'a tare da taimakon Musulunci. Shi kuma Sarki ya bukaci Al-Maghili da ya zauna a fada domin ya dinga warware al'amuran da suka shafi shari'a. Wannan ya bawa malamin damar rubutawa Sarkin Kano Muhammadu Rumfa wasu litattafai akan gudanar da mulki.

Ance lokacin da Imam al-Suyudi yazo Kano daga Misra, Sarki Rumfa ya nemi malamin akan yayi masa addu'a kan duk Sarkin da aka nada sai an hada kiran sa tare da sunan sa. Kuma addu'ar tayi tasiri har yanzu lakabi da kirarin da ake yiwa Sarkin Kano shine "Magajin Rumfa". Haka kuma Sarki ya sake cewa Imam al-Suyudi ya yi masa addu'a cewa, "Duk wanda yazo Kano Allah yayi masa arziki, to ya yi zaman sa a Kano kada ya koma garin su". Wannan addu'a tayi tasiri domin a yanzu mafi yawancin masu zuwa Kano neman arziki basa komawa garin su.

An ce addu'o'i tara Sarki Rumfa ya roki Malam al-Suyudi ya yiwa Kano domin neman albarka ga wannan gari. Kuma kowacce addu'a aka yi sai Sarki ya kawo sadaka mai yawa ya bashi, sannan za'a kuma yin wata. A

Bunkasar Kasuwanci 

A zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne Kano ta fara bunkasa ta fannin Kasuwanci ta fannin hada-hadar abubuwan da ake sarrafawa a Kano. Wannan dalili ya janyo zuwan baki daga nahiyoyi daban-daban domin su kawo kayan su domin siyarwa, kuma suma su sayi kayan da Kanawa suke sarrafawa.

Babban abin da Sarki Rumfa yayi shine sai ya bayar da umarnin bude kasuwa wadda yan kasuwa za su dinga hada-hadar kasuwancin su a ciki. Wannan kasuwa da aka bude ita ce Kasuwar Kurmi wadda ta zama babbar kasuwa a fadin Kasar Hausa. Wannan dalili ya janyo zuwan yan kasuwa Larabawa daga yankin Africa ta Arewa. Hakan ya bunkasa Kano a matsayin cibiyar Kasuwanci ta kasar Hausa a lokacin zamanin Cinikayya ta Cikin Sahara wato "Trans-Saharan Trade" a turance.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu