ZUWAN AL-MAGHILI KANO

Sheikh Al-Maghili

Sheikh Muhammad bin Abdul-Karim Al-Maghili ya kasance wani shahararren malamin addinin Musulunci kuma Sharifi dan asalin garin Tilimsan dake yankin kasar Algeria a yanzu. Sheikh Al-Maghili ya yi aikin yada addinin Musulunci a yankuna dake cikin Sahara da kuma yammacin Africa kamar kasar Hausa.

A kasar Hausa Sheikh Al-Maghili ya ziyarci birnin Kano, kuma zuwan sa ya yi tasiri kwarai da gaske ta hanyar ci gaban addinin Musulunci da kuma mulki a Kano.


Zuwan sa Kano

Sheikh Muhammad bin Abdul-Karim Al-Maghili yazo Kano ne a cikin karni na sha biyar '15th century ' a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499). Kamar yadda Wazirin Kano Alhaji Abubakar Dokaji ya kawo a littafin sa mai suna 'Kano ta Dabo Ci Gari " ya ce babban dalilin zuwan Sheikh Al-Maghili zuwa Kano shine yayi mafarki da Annabi (SAW) yace da shi "Kaje Yamma ka karfafa Musulunci". Da tashin sa daga  barcin sai ya debi kasar Madina ya kunshe a adiko ya yiwo yamma. Duk garin da yazo sai ya gwada kasar garin da ta Madina wacce ke kunshe cikin adikon sa, amma sai yaga ba iri daya bace. Yana haka har ya iso Kano. Da dai ya gwada kasar sai ya ga tayi daidai da ta Madina. Sai yace "Ashe nan ne inda Annabi (SAW) yace in zo".

Lokacin da Sheikh Al-Maghili yazo Kano ya himmatu wajen gudanar da aikin koyar da addinin Musulunci tare. Wannan dalili yasa Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya gayyace shi zuwa fadar sa domin ya zama Malami mai bayar da fatawa akan Shari'a. A wannan lokaci malamin ya bukaci Sarki Rumfa da ya gina Masallacin Jama'a domin a dinga taruwa ana yin Sallah.

A bangaren mulki kuma, Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya bukaci Sheikh Al-Maghili ya rubuta masa wasu ka'idojin mulki domin samun nasara a mulkin sa. Don haka ne malamin ya rubutawa Sarkin Kano Rumfa wata 'Risala' ta sha'anin sarauta wadda a cikin ta ya bayyana irin abubuwan da suka kamaci Sarki. Wadannan ka'idojin ne Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya nakalta suka zama al'ada a wurin Sarakunan Kano zuwa yau. Irin al'adun sune kamar haka:

  1. Sarki ya dinga yin zaman harde akan karaga sa'adda ake shari'a
  2. Sarki ya takaita motsi idan yana kan karaga
  3. Sarki ya takaita magana sai ta zama dole

Wadannan ka'idoji da sauran wasu, sune Sheikh Al-Maghili ya rubutawa Sarkin Kano domin samun nasara a mulkin sa.

A takaice dai wannan Risala ta kasu zuwa manyan litattafai guda uku wanda Sheikh Al-Maghili ya hade su ya rubutawa Sarkin Kano Muhammadu Rumfa kamar haka:

  1. Tajulmulk fi ma Ya jibbu alal muluki (Kambin sarauta a kan abin da ya wajaba ga sarauta)
  2. Majmu'at Al-Maghili fi shu'unin al-imarati (Talifin Al-Maghili a cikin sha'anonin sarauta)
  3. Ma Yajuz ala al-Hukkami fi Rad'i Nasi an al-Haram (Abin da ya halatta kan masu hukunci don tsawatar da mai rabkana akan cin haram)

Sarkin Sharifai

Lokacin da Sheikh Al-Maghili zai koma gabas ya bar yayan sa guda uku a Kano cikin su akwai Malam Isa wanda ake kira Sidi Fari. Ya bar masa carbi, da takobi da Al-Qurani da sanda da mizani. Tun lokacin sa ne Sharifai ke zama a fadar Sarkin Kano a lokacin gudanar da Shari'a. Kuma daga sunan dan nasa Sidi Fari ne aka samo sunan sunan sarautar Sharifai. Har zuwa yau Sarkin Sharifai a Kano yana fitowa ne daga zuriyar Sheikh Al-Maghili.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu