Zanen Shehu Usman Dan Fodio. yaqeeninstitute.org |
Kamar yadda tarihi ya tabbatar, Musulunci yazo kasar Hausa tun cikin karni na sha hudu wato 14th century a turance. Musulunci ya fara karbuwa ne a manyan biranen kasar Hausa irin su Kano da Katsina. Tun daga wannan lokaci Musulunci ya barbazu a cikin fadin kasar Hausa inda sarakuna da talakawa suka karbi addinin tare da aiwatar da shi bisa sharuddan sa.
Sai dai da tafiya tayi fara yin nisa, sai sarakuna da talakawa suka dawo suna gauraya Musulunci da akidoji da al'adun irin su tsafi da bori. Haka kuma sarakuna a kasar Hausa ta wani gefen suka koma suna zalunce-zalunce tare da tsananta wa talakawa musamman ta bangaren biyan haraji. Wadannan dalilai suka janyo lalacewar zamantakewa a fadin kasar Hausa har ta kai wasu mutane sun fara neman mafita daga wannan hali.
Bayyanar Usman Dan Fodio
Shehu Usman Dan Fodio ya fito ne daga cikin kungiyar Fulani ta Torankawa wato kenan shi 'Batoranke' ne. An haife shi a garin Maratta cikin kasar Gobir a shekarar 1754 Miladiyya. Shehu Usman ya zauna a gurare daban-daban domin neman ilmin addinin Musulunci. Daga baya ya zauna a Degel inda ya fara wa'azi akan jaddada addinin Musulunci. A zamanin Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo, ilmin Shehu Usman da takawar suka fara bayyana a sarari kuma ya kara bada karfi wajen koyarwa da wa'azi.
Haka kuma a wannan karnin ne labarin wa'azin Shehu Usman Dan Fodio ya fara habaka yana bazuwa tare da labarin dinbin karatun sa da ilmi. Haka kuma karamomin sa da nuna gaskiyar sa da bajintar sa da mutuncin sa suka bazu ko'ina a fadin kasar Hausa. Wannan dalili ne yasa Shehu ya dinga samun almajirai daga fadin kasar Hausa suna zuwa domin daukar karatu a gaban sa.
A daya hannun kuma Sarkin Gobir Bawa ya fara kin Shehu sakamakon yadda yake samun shahara a koda yaushe. Kullum almajiran sa sai karuwa suke daga kowanne bangare. Don haka sai Sarkin Gobir Bawa ya fara shiryawa Shehu makirce-makirce don ya halaka shi. An ce wata rana Sarkin Gobir Bawa ya gayyaci Shehu tare da wasu daga cikin malaman kasar Hausa zuwa wani biki. Haka kuma a wannan bikin Sarki Bawa ya gayyaci bokaye da masu bautawa dodanni da iskoki. Ya raba kyaututtuka inda ya bawa Shehu kyautar awo biyar na zinari, amma Shehu yaki karba yace baya so. Kawai dai Shehu yace yana gabatar da wasu bukatu ga Sarki Bawa kamar haka:
- Shehu ya bukaci Sarki ya tuba ya dawo kan tafarkin addinin Musulunci. Ya daina tsafi da kuma mu'amula da bokaye.
- Shehu ya bukaci abar shi da jama'ar sa su ci gaba da wa'azin addinin Musulunci ba tare da kuntatawa
- Shehu ya bukaci a bar mutane suyi addinin Musulunci kamar yadda Allah ya umarta
- A saki mutanen da aka daure saboda suna yin wa'azi
- A rage harajin da aka dorawa talakawa
Daga karshe dole Sarkin Bawa ya yarjewa Shehu wadannan bukatu. Sai dai kuma bayan mutuwar Sarki Bawa, sai wanda aka nada ya gaje shi ya zama Sarkin Gobir wato Yakubu ya tayar da dukkan wadannan alkawura wadanda Sarkin Gobir Bawa yayi da Shehu. Kuma yaci gaba da matsawa Shehu fiye da da, har shima ya rasu aka sake nada wani sabon Sarkin Gobir din wato Sarkin Gobir Nafata. Shima dai Sarki Nafata ya ci gaba da matsawa Shehu Usman Dan Fodio, har ma ya sanyawa Shehu wasu dokoki kamar haka:
- Daga yau bayan Usman dan gidan Fodio kada wanda ya sake yin wa'azi
- Kada wanda ya shiga addinin Musulunci idan bai gada ba
- Daga yau kada kowa ya sake nada rawani
- Haka kuma kada mata rika yin lullubi
Haka Sarki Nafata ya ci gaba da kuntatawa Shehu da mabiyan sa har shima ya rasu aka nada sabon Sarkin Gobir mai suna Yumfa. Shima dai Sarkin Gobir Yumfa ya dora wajen kuntatawa Shehu da mabiyan sa. Har akwai lokacin da Sarki Yumfa yasha aikawa Shehu da mahara har gidan sa na Degel don su yake shi, amma Shehu yayi galaba akan su ya koro su. Daga nan sai Sarkin Gobir Yumfa ya sake dabara, ya aikawa Shehu yazo yana son ganin sa. Ashe yasa a haka rijiya a cikin fadar sa aka kakkafa masu a cikin ta aka kawo babbar tabarma aka rufe bakin ta. Da Shehu yazo sai Yumfa yayi masa ishara da hannu wai ya hau kan tabarma. Shehu ya tafi gaba-gadi ya zauna, yan rakiyar sa Abdullahi da Almar suka zauna gefen sa wato a hagun sa da daman sa. Da Yumfa yaga ba abin da ya sami Shehu, sai ya dauko bindiga ya nufi Shehu ya harbe shi, amma abin al'ajabi sai bindigar ta juya ta harbi daya daga cikin fadawan Yumfa. Nan take Yumfa yace wa Shehu "je ka naji, daga yau na haramta maka zama a kasata, kai da iyalan ka, kuma kada in ji wasu sun bika. Shehu yace hakika zan bar kasar nan taka, amma ka sani bazan rabu da jama'ata ba, duk musulmi mai son bi na ba zan hana shi ba".
Kaddamar da Jihadi 1804-1807
Lokacin da Shehu Usman ya dawo gida sai ya tara jama'ar sa yace: "Ya ku jama'a yau tura ta kai bango, zalunci da kaskancin shugabanni kasa ya ishe mu. Na umar ce ku kuyi tanadin makamai don kare kan mu, mu tashi tsaye mu ci gaba da bautawa Allah ko da zamu bayar da rayuwar mu ne, babu sauran kauna tsakanin mu da kafirai". Bayan wannan jawabi sai Shehu Usman Dan Fodio ya yayi shiri tare da mabiya masu yawa suka yi kaura zuwa wani gari da ake kira Gudu.
Bayan Shehu ya koma Gudu, sai Sarkin Gobir Yumfa ya ci gaba da matsawa mutanen Shehu wanda suka saura a cikin kasar Gobir. Haka kuma Sarki Yumfa yayi shiri domin kaiwa Shehu harin yaki. Shima Shehu sai daura shirin yaki ya tunkari kasar Gobir. A tsakanin Shekarar 1804 zuwa 1807 Shehu ya kaddamar da Jihadi. An ce da Shehu ya fara cin kauyukan Gobir da yaki har sai dai yakai ga babban birnin su na Alkalawa. Aka gwabza yakin da basu taba yin irin sa ba har Shehu da mayakan sa suka sami damar kutsawa cikin fadar Sarkin Gobir Yumfa suka kashe shi. Wannan nasara ya ta bawa Shehu Usman Dan Fodio damar kwace ikon mulkin kasar baki daya da yardar Allah. Daga nan mulkin Fulani ya kafu a fadin kasar Hausa da sauran wasu yankuna dake Arewacin Nigeria a yanzu. Wato dai yanzu an samu Daular Musulunci kenan karkashin jagorancin 'Amirul Muminin ' wato 'Sarkin Musulmi '.
Fadin girman Daular Sokoto. Source:creativecommons.org |
Bayan nasarar Shehu akan Sarkin Gobir Yumfa, sai kabilun Fulani da sauran al'umma a kasar Hausa da sauran yankuna suka dinga tura jagororin su domin karbo tutar Jihadi wadda su ma zasu kaddamar a yankunan su. Don haka Shehu Usman Dan Fodio ya bayar da tutar Jihadi ga Masarautu guda goma sha uku tare da umartar su wajen jaddada addinin Musulunci da kuma kafa mulki bisa shari'ar Musulunci. wadannan masarautu da aka bawa tutar Jihadi sune kamar haka:
- Malam maru Dallaji a Katsina
- Malam Sulaimanu a Kano
- Malam Isiyaku a Daura
- Malam Musa a Zaria
- Malam Yakubu a Bauchi
- Malam Buba Yero a Gombe
- Malam Modibbo Adama a Adamawa
- Malam Sambo a Hadeja
- Malam Zaki a Katagum
- Malam Gwani Mukhtar a Misau
- Malam Dantunku a Kazaure
- Malam Dendo a Nupe
- Malam Alimi a Ilorin
Wadannan tutocin Jihadi sune wadanda Shehu Usman Dan Fodio ya bawa manyan jagororin al'umma domin su kaddamar da Jihadi a yankin su.
0 Comments