Ganuwar birnin Kano a shekarar 1903 |
Ganuwar birnin Kano wata babbar Katanga ce mai tsohon tarihi wadda Sarakunan Kano suka gina ta domin bawa birnin kariya musamman saboda yanayin yake-yake da ake yi a wannan lokaci. Ganuwar birnin Kano tana daya daga cikin abubuwan tarihi wanda Kano take alfahari da su. An shafe fiye da karni bakwai wato fiye da shekara dari bakwai ana ginin Ganuwar Kano kafin a gama ta.
Karni na Sha Daya (11th Century)
Wannan Ganuwa ko Katanga mai tsohon tarihi Sarkin Kano Gijimasu dan Sarkin Kano Warisa ne ya dasa harsashin gina ta a farkon karni na sha daya wajejen shekarar 1095 Miladiyya. An fara ginin daga wani waje da ake kira Rariya (tsakanin Kofar Dan Agundi da Kofar Na'isa). An ce a ranar farko da aka fara ginin, Sarki ya yankawa maginan har shanu dari.
Karni na Sha Hudu (14th Century)
Amma ba'a kare ginin ba sai a cikin zamanin Sarkin Kano Usman Zamna Gawa, wato cikin karni na sha hudu wato 14th century a turance. Ginin ya ci gaba zuwa Kofar Mazugal zuwa Kofar Adama. Daga nan gini ya tafi zuwa Kofar Gudan, daga nan zuwa Kofar Waika zuwa Kofar Kansakali, daga har aka iso Kofar Tuji. Amma ya kamata mai karatu ya sani cewa a yanzu babu Kofar Tuji, Kofar Adama, da fatan kuma Kofar Gudan.
Karni na Sha Biyar (15th Century)
A cikin Karni na sha biyar a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499) an yi karin Ganuwar Kano inda aka shigo da Fadar Masarautar Kano ta yanzu cikin gari. A lokacin da aka fara ginin ganuwar, Fadar Sarkin Kano tana wajen Ganuwa ne. Haka kuma Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya bada umarni inda aka kara Ganuwar Kano tun daga Kofar Dagaci zuwa Kofar Mata, zuwa Kofar Nassarawa. Sannan daga Kofar Dogo zuwa kan iyakar Kofar Kansakali.
Karni na Sha Bakwai (17th Century)
A cikin karni na sha bakwai a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Na Zaki (1618-1622) an yi karin Ganuwar Kano don kara fadada da'irar birni saboda yawan hare-hare da Katsinawa da Kwararrafawa da mutanen Borno suke ta kawo wa Kano da kewan ta. An fara karin Ganuwar daga kan iyakar Kofar Dogo (Kofar Na'isa a yanzu) zuwa Kofar Gadon Kaya, zuwa Kofar Dukawuya har zuwa Kofar Kabuga zuwa iyaka Kansakali.
Kamar yadda Kundin Tarihin Kano na "Kano Chronicle" ya tabbatar da cewa wani Hakimin Sarki Muhammadu Na Zaki mai suna Wambai Giwa ne ya dauki gabarar aikin, wato shine ya dauki hidimar aikin ginin. A lokacin ginin, a kullum Wambai Giwa yakan kimanin shanu hamsin tare da kabakin abinci ga maginan. Haka kuma ya dauki nauyin malamai masu yin addu'a domin samun tsaro ga birnin Kano. Sakamakon wannan hidima ta Wambai, Sarkin Kano Muhammadu Na Zaki yayi farin ciki har Sarki ya bawa Wambai Giwa sarautar Karaye wato ya nada shi Sarkin Karaye.
0 Comments