![]() |
| Wasu daga cikin Kofofin birnin Kano. Daga sama hagu zuwa dama ; Kofar Waika, Kofar Mazugal, Kofar Ruwa. Daga kasa hagu zuwa dama; Sabuwar Kofa, Kofar Gadon Kaya, Kofar Dan Agundi |
Kamar yadda muka yi bayanin yadda aka gina Ganuwar Kano, to haka kuma akwai kofofi daban-daban da suke a bangarori daban-daban na ita Ganuwar. A yanzu akwai kofofin shiga birnin Kano har guda Goma Sha biyar. Akwai wata waka da Alhaji Ahmad Bahago ya kawo a littafin sa mai suna "Kano Ta Dabo Tumbin Giwa: Tarihin Unguwannin Kano da Mazaunanta da Ganuwa da Kofofin Gari" ya zayyano kofofin shiga birnin Kano a waka kamar haka ;
"Ta Kansakali ta Kabuga, Gadon Kaya Dukawuya. Adama Kofar Ruwa, Mazugal Wamban Kano. Ta Nassarawa, Dan Agundi Na'isa Kofar Midil. Kofar Waika ga Dawanau mun zagayo Kofar Famfo duka"
![]() |
| Taswirar Ganuwar Kano da Kofofin ta |
A takaice dai birnin Kano yana da kofofin shiga cikin birni har guda goma sha biyar. Ga jerin Kofofin da kuma shekarar da aka gina su kamar haka:
- Kofar Kansakali (1112 A.D.)
- Kofar Waika (1112 A.D.)
- Kofar Dawanau (1112 A.D.)
- Kofar Ruwa (1112 A.D.)
- Kofar Mazugal (1112 A.D.)
- Kofar Wambai (1112 A.D.)
- Kofar Mata (1461)
- Kofar Nassarawa (1463)
- Sabuwar Kofar (1934)
- Kofar Dan Agundi (1463)
- Kofar Na'isa (1470)
- Kofar Gadon Kaya (1619)
- Kofar Famfo (1928)
- Kofar Dukawuya (1621)
- Kofar Kabuga (1621)


0 Comments