TARIHIN KOFAR MAZUGAL

Kofar Mazugal 

An gina Kofar Mazugal a cikin karni na sha biyu wato 12th century a zamanin Sarkin Kano Gijimasu dan Warisa (1095-1134). Tana cikin kofofin farko da Sarki Gijimasu ya gina, wato dai tana cikin kofofin farko a Kano.

Kamar yadda Alhaji Ahmad Bahago ya kawo a littafin na Tarihin Ganuwa da Kofofin Kano yace asalin Mazaunan cikin Kofar Mazugal sun kasance makera da suka shahara wajen sana'ar su. Sukan kera dukkan kayan da ake amfani da su musamman kayan yaki wanda akan zo daga ko'ina domin sayen makamai a wajen su. Tun da yake makeran kewayen suna da yawa, don haka dole a samu zuga-zugai masu yawa. Wadannan zuga-zugai su ake kira "Mazugai", har kuma suka zama ana kiran su Mazugal. Don haka ne mutane suka fara kiran kofar da suna "Kofar Mazugal", wato dai daga Mazugai ko Zuga-zugai. A wani kaulin kuma ance wai Kofar Mazugal ta samo sunan ta ne daga sunan wani bamaguje mai suna "Mazugal" wanda yake zaune a kusa da Kofar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu