TARIHIN KOFAR RUWA

Kofar Ruwa

Ita ma dai Kofar Ruwa tana cikin kofofin farko a birnin Kano wanda aka gina a cikin karni na sha biyu a zamanin Sarkin Kano Gijimasu (1095-1134) lokacin da ya fara gina Ganuwar Kano.

Asalin sunan Kofar Ruwa shine "Kofar Adama", sannan " Kofar Lunkwi", sannan daga baya ta koma Kofar Ruwa. Da farko dai ance Lunkwi wani Sarkin Kofa ne da ya sarauci kofar tun da can, don haka ne ake kiran kofar da sunan sa. Amma daga baya an canza sunan Kofar zuwa Kofar Ruwa. Asalin abin da ya faru ance wata rana ruwa yayi ambaliya har ya karya garu daga gabas da Kofar Lunkwi. Bayan da ruwa ya janye, sai mutane suka rika shigewa ta cikin ta kuma suka rika kiran ta da "Kofar Ruwa" saboda ruwa ne ya yi ta.

A zamanin shekarun baya, kewayen Kofar Ruwa guri ne mai yawan ruwa da fadamu. Dona haka aka dinga yin noman rake a kewayen wannan Kofa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu