![]() |
Kofar Dawanau |
Ita ma dai Kofar Dawanau tana cikin kofofin farko wanda aka fara ginawa a Kano. Sarkin Kano Gijimasu dan Warisa (1095-1134) ne ya gina ta a cikin karni na sha biyu.
An ce asalin sunan Kofar Dawanau shine "Kofar Dankwai". Shi kuma Dankwai an ce shima wani bamaguje ne wanda yake zaune a kusa da wannan Kofa. An ce Sarkin Kano Muhammadu Kisoki ne ya canza sunan Kofar daga Kofar Dankwai zuwa "Kofar Dawanau". Shi kuma Dawanau ya kasance wani mutum mai arziki kuma abokin Sarki Kisoki. Don haka ne Sarki ya mayar da sunan Kofar zuwa Dawanau DOMIN girmamawa ga abokin nasa. Garin Dawanau ya samo sunan sa ne daga wannan kofa, saboda Kofar tana daidai da garin Dawanau a wannan lokaci.
Tarihi ya tabbatar da cewa ta Kofar Dawanau ne Larabawa da mutanen Nijar suke shigowa Kano tun a zamanin da domin yin kasuwanci.
0 Comments