Kofar Waika |
Sarkin Kano Gijimasu dan Warisa (1095-1134) ne ya gina wannan kofa a cikin karni na goma sha biyu. Kamar yadda Alhaji Ahmad Bahago ya rawaito a littafin sa na Tarihin Ganuwar Kano da Kofofin ta, ance akwai wata tsohuwar rijiya wadda saboda dadewar ta ba'a san lokacin da aka haka ta ba. Ita wannan rijiya sunan ta "Waika", kuma tana kusa da Kofar. Saboda haka wannan kofa ta sami sunan "Kofar Waika" saboda sunan wannan rijiya. A da can Azbinawa mutanen cikin Sahara suna bai wa rakuman su ruwa a wannan rijiya idan sun shigo Kano domin kasuwanci. Kuma har yanzu akwai kufan wannan rijiya.
Kuma tarihi ya tabbatar da cewa ta Kofar Waika ne Sarkin Kano Tukur ya fita daga birnin Kano a lokacin Yakin Basasar Kano (1893-1894), fitar da bai dawo ba. Don haka wasu suka camfa Kofar da cewa duk Sarkin da ya fita ta kofar ba zai dawo ba.
0 Comments