Kofar Kansakali |
Ita mai dai Kofar Kansakali tana daya daga cikin Kofofin farko a birnin Kano. Ita ma dai Sarkin Kano Gijimasu dan Warisa ne ya gina ta a karni na goma sha biyu.
Kamar yadda tarihi ya tabbatar, an ce akwai wani shahararren makeri da ya zauna a wannan kofa yana kirar takubba wato "Kansakali". Don haka ne mutane idan za su je gurin sa sai su dinga cewa "mun tafi gurin mai Kansakali", da haka a ne sunan ya samu har mutane suke kiran kofar da suna "Kofar Kansakali".
A da mutane daga yammacin Kasar Hausa wajejen Sokoto idan za su tafi aikin Hajji a wannan kofa suke yin Zango. Kuma idan sun tafi sukan fita ta Kofar Wambai domin kofa ce da tayi saiti daidai da ta Wamban.
0 Comments