TARIHIN KOFAR KABUGA

Kofar Kabuga 

Sarkin Kano Muhammadu Na Zaki dan Sarkin Kano Zaki (1618-1623) shine ya gina Kofar Kabuga a cikin karni na goma sha bakwai wato 17th century a turance.

Kauli na farko yace gurin da Kofar Kabuga take guri ne da ya shahara da noman lalle. An manoman lalle a gurin sukan bushewa tare da bugawa idan ya bushe. Haka kuma ance bayi sukan fanshi kan su da bugun lalle a wannan waje. Akan basu aikin lalle na wani adadi na shekaru ko watanni. Idan sun cika adadin sai a yanta. Wasu kuma akan dauke su aikin bugun lallen suyi a biya su. Wanda ya gama nasa aikin yakan je ya gaya wa Sarkin Kofa. Shi kuma Sarkin Kofa yakan tambaye shi cewa: "Har ka buga", daga sai Sarkin Kofa ya sallame shi. Da haka wannan Kofa ta sami sunan Kabuga.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu