Kofar Dukawuya |
Ita ma dai Kofar Dukawuya tana cikin Kofofin da Sarkin Kano Muhammadu Na Zaki ya gina a cikin karni na sha bakwai. Akwai kauli guda biyu dangane da asalin yadda sunan Kofar Dukawuya ya samo asali.
Kauli na farko yace a da can duk mutumin da zai shige ta wannan kofa idan yana dauke da wani abu sai ya bada na Sarkin Kofa kafin ya shige. Wata rana sai abokin wasan Sarkin Kofa yazo da kara a kan sa zai shige ba tare da ya bada komai ba. Sai Sarkin Kofa yace sai lallai ya bayar zai shige. Cikin barkwanci sai suka kama kokawa, sai Sarkin Kofa ya doke shi da kafa a wuya. Sai abokin yace "Kofar taka ta zama ta duka wuya". Saboda wannan yasa mutanen da suke gurin suka dinga kiran kofar da suna "Kofar Dukawuya".
A kauli na biyu kuma an ce Kofar Dukawuya ta samo asalin sunan ta ne daga sunan wani mutuma da ake kira Daukawuya. Daukawuya an ce wani kakkarfan mutum ne manomi wanda gidan sa yake dab da wannan kofa. Irin amfanin gonar da yake daukowa a wuyan sa ba kowanne kato ne zai iya dauka ba. Wannan dalili yasa ya a dinga kiran sa da suna "Daukawuya". Kasancewar Kofar kusa da gidan sa. Sai aka dinga kiran kofar da suna "Kofar Daukawuya" daga baya kuma ta zama "Kofar Dukawuya".
Tarihi ya tabbatar da cewa ta wannan Kofa ta Dukawuya ne Turawa suka shiga cikin birnin Kano bayan suka cinye Kano da yaki a shekarar 1903. An ce lokacin da suka iso Kofar Dukawuya sun tarar da ita a rufe, don haka suka yi amfani da babbar bindigar su suka fasa kyauren Kofar wanda ya kasance na fata da karfe.
0 Comments