Kofar Gadon Kaya |
Sarkin Kano Muhammadu Na Zaki (1618-1623) ne ya gina wannan Kofa ta Gadon Kaya a cikin karni na sha bakwai wato 17th century a turance. Akwai kauli guda biyu dangane da asalin yadda sunan Kofar Gadon Kaya ya samo asali.
Kauli na farko yace akwai wani Sarkin Kofa da aka taba yi mai kula da Kofar. An ce yakan kewaye gadon sa da kaya yana kwanciya a tsakiya. Duk lokacin da kaya ta soke shi, sai ya farka daga bacci. Yayi haka ne don kada ya shagala da bacci har ya kasa tsaron Kofar. Don haka ne mutane suka fara kiran kofar da suna "Kofar Mai Gadon Kaya" har kuma daga baya ta koma "Kofar Gadon Kaya".
A wani kaulin kuma ance akwai wani manomin kayan lambu mai suna Isma'ila wanda yake da gida kusa da wannan Kofa. Shi wannan mutum ana yi masa kirari da cewa shi Gadon Kaya ne, wato kowa ya hau shi sai ya soke shi. Saboda yana zaune kusa da kofar, sai aka dinga kiran Kofar da sunan "Kofar Gadon Kaya".
Kofar Gadon Kaya a cikin shekarar 1903 |
Domin karin bayani akan tarihin Kofar Gadon Kaya, ku danna bidiyo ta kasa.
0 Comments