Kofar Na'isa |
Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499) ne ya gina wannan kofa ta Na'isa a cikin karni na goma sha biyar. A da wannan kofa babu ita, asalin kofar sunan ta "Kofar Dogo" wadda take can wajen Hauren Shanu dake tsakanin Kofar Gadon Kaya da Kofar Na'isa a yanzu.
Ita Kofar Na'isa ta maye gurbin Kofar Dogo ne. Yadda aka yi Kofar Na'isa ta maye gurbin Kofar Dogo shine wani babban ayari na Fulani baki sun zo da dabbobin su a karni na goma sha tara zamanin Sarkin Kano Sulaimanu (1807-1819) sai aka hana su shigowa ta Kofar Dogo. Don haka sai suka matsa gaba suka sara garu suka shigo cikin gari suka baza dabbobin su suna ta kiwo. Ganin haka sai Sarkin Kofa yaje ya gaya wa Sarki Sulaimanu abin da ya faru. Da aka kai su gaban Sarki sai ya tambaye su dalilin da yasa suka sara garu, sai shugaban Fulanin yace "Don na isa ne" wato dai yana nufin tun da Sarki Bafillace ne, su ma Fulani ne, don haka sun isa kenan tun da yan uwan sa ne Fulani. Jin haka sai Sarkin Kano yace "Lallai ka isa". Daga wannan lokaci Sarkin Kano Sulaimanu ya bayar da umarni aka toshe Kofar Dogo, aka gyara wannan kofa da Fulani suka sara, wato Kofar Na'isa ta yanzu. Aka saka mata kyaure tare da saka makulli kwado na gargajiya wanda har yanzu yana nan.
Kofar Na'isa cikin shekarar 1975 Domin samun karin bayani akan tarihin Kofar Na'isa, ku latsa bidiyon kasa: |
0 Comments