TARIHIN KOFAR DAN AGUNDI

Kofar Dan Agundi 

An gina wannan Kofa ta Dan Agundi ne a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa cikin karni na sha biyar. A da can ana kiran kofar da sunan "Kofar Yayan Sarki", saboda ta wannan kofa suke yawan shigewa idan za su je gidan Sarki na Gandun Albasa, wato Gandun Sarki.

Ga yadda aka samo sunan "Kofar Dan Agundi". Ance a zamanin Sarkin Kano Ibrahim Dabo (1819-1846) an ginawa yayan Sarki gidaje a kusa da Kofar. To akwai wata mata mai suna Agundi wadda take sayar da kaya a gindin wata kuka kusa da Kofar. Duk lokacin da Sarkin Kano Dabo yazo ganin gini, sai ta taso tayi ta yiwa Sarki guda. Wannan abu yana burge Sarki sosai. Don haka ne lokacin da aka gama ginin yayan Sarki, sai yace "Da a ce wannan mace namiji ce, da nayi mata sarautar kofar 'yayan Sarki '. Sai bayin Sarki suka ce, ai tana da da namiji. Don haka sai Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya nada dan ta Sarkin Kofa. Daga nan mutane suka rika kiran Kofar da sunan "Kofar Dan Agundi".

Kofar Dan Agundi cikin shekarar 1980

Domin samun karin bayani akan tarihin Kofar Dan Agundi, ku latsa bidiyon kasa domin kallo:



Post a Comment

0 Comments

Close Menu