Kofar Nasarawa |
Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya gina wannan kofa a cikin karni na goma sha biyar. An ce ta samu sunan "Nasarawa" ne saboda ta nan ne Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi (1855-1882) yake shigewa idan za shi gidan sa na Nasarawa. Kuma an ce duk lokacin da yaje yaki ya samo nasara to ta wannan Kofa yake shigowa cikin birnin Kano.
Tun zamanin da Turawa suka zo Kano, Kofar Nasarawa ya zama wata Kofa wadda mutane suke mata kirari da "Kofar Mulki". Domin kuwa idan Sarkin Kano za shi gidan Gwamnati domin gaisawa da Razdan ta wannan Kofa yake fita. Haka shima Razdan idan zai kawo wa Sarki ziyara ta wannan Kofa yake shigowa. A wannan zamanin kuma wannan alaka ta mulki ta koma tsakanin Gwamna da Sarki.
Domin samun karin bayani akan tarihin Kofar Nasarawa, ku latsa bidiyon kasa:
0 Comments