Kofar Mata |
Tarkin Kano Muhammadu Rumfa shine yayi wannan Kofa a cikin karni na sha biyar.
Dalilin da yasa kiran kofar Mata da sunan an ce ta wannan kofa ne matan Sarki suke fita zuwa Fanisau, duk lokacin da Sarki ya tafi Fanisau. Idan matan za su shige sai an kori duk mutane dake bakin Kofar domin matan su shige. An ce shine dalilin da yasa ake kiran Kofar da suna "Kofar Mata".
Tarihi ya tabbatar cewa ta Kofar Mata Sarkin Kano Alu (1894-1903) ya fita ya bi Damagarawa zuwa Gezawa inda aka gwabza yaki. Bayan gama yaki sai wasu Damagarawa mazan su da matan su suka zo daidai wannan Kofa daga wajen garu suka taru. Da Sarkin Kofa yaje ya tambaye su dalilin taruwar su, sai suka ce su yan gudun hijra ne, saboda yunwa baza su iya komawa gida ba. Sai Sarkin Kofa yaje ya gaya wa Sarkin Kano Alu, shi kuma Sarki yasa aka rika aiko musu da abinci. An ce wadannan mutane da suka yiwo gudun hijra sune ainihin mutanen da suka fara zama a Fagge.
0 Comments