Kofar Wambai |
An gina wannan Kofa tun cikin karni na sha biyu a zamanin Sarkin Kano Gijimasu dan Warisa. Kenan tana daya daga cikin Kofofin birnin Kano na farko.
Kofar Wambai ta samu sunan ta ne daga sunan wani shahararren hakimin Sarkin Kano Muhammadu Na Zaki mai suna Wambai Giwa. Shi kuma Wambai Giwa an ce gidan sa yana kusa da wannan kofa. Don haka mutane suka dinga kiran kofar da suna "Kofar Wambai" wato Wambai Giwa. Amma an ce asalin sunan Kofar "Kofar Rariya"
A tarihi an ce a tsakanin Kofar Wambai da Kofar Mata ne Sarkin Damagaram Amadu Kuren-Daga yayi sansani yana nufin shiga cikin birnin Kano da yaki ko ta halin kaka.
0 Comments