Kofar Famfo |
Kofar Famfo tana daya daga cikin Kofofin da aka gina lokacin Turawan Mulkin Mallaka. An sara Kofar ne a zamanin Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero a shekarar 1928. Dalilin sara Kofar shine saboda ana aikin shigo da ruwan famfo da lantarki zuwa cikin birnin Kano daga Challawa. Don haka bayan an fitar da Kofar sai mutane suka saka mata sunan "Kofar Famfo" saboda wannan dalili.
Kuma ta dalilin bude Kofar Famfo ne aka yi hanyar titi daga Gwauron Dutse zuwa Chalawa domin shigo da bututun ruwa zuwa gidan ruwa na Gwauron Dutsen.
0 Comments