Sabuwar Kofa |
Ita ma dai Sabuwar Kofa tana daya daga cikin Kofofin da aka gina a zamanin Turawan Mulkin Mallaka. An gina ta ne cikin shekarar 1934 a zamanin Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero (1926-1953).
Dalilin gina Sabuwar Kofa shine cewa a cikin shekarar 1927 an gina Makarantar Midil wadda yanzu ake kira "Rumfa College". Saboda a saukakawa dalibai fitowa daga cikin birnin Kano domin zuwa Makarantar Midil, sai Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ya bayar da umarnin sara ganuwa wadda ta nan dalibai suke fitowa zuwa Makaranta. Dalilin wannan ne mutane suke kiran Kofar da suna "Kofar Midil" daga baya kuma ta koma Sabuwar Kofa.
Hoton Sabuwar Kofa da daddare |
Domin samun karin bayani akan tarihin Sabuwar Kofa, ku latsa bidiyon kasa:
0 Comments