Masu Jihadi |
Addinin Musulunci ya shiga kuma ya barbazu a kasar Hausa ciki har da Kano kamar yadda muka bayyana a baya. Mutane sun ci gaba da aiwatar da shi bisa sharuddan sa. Sai dai bayan wani zamani, mutane sun dawo suna gauraya Musulunci da akidoji da al'adun da suka ci karo da koyarwar addinin Musulunci. Haka kuma a wani bangaren sarakuna sun koma WA zalunce-zalunce tare da tsananta wa talakawa ta hanyoyi da yawa kamar karbar haraji.
A Kano harkoki sun fara dagulewa a lokacin Sarkin Kano Muhammadu Sharefa wanda yayi mulki daga shekarar 1703 zuwa 1731. Haka kuma Sarkin Kano Kumbaru (1731-1743) an ayyana cewa saboda tsanani a Kano takakawa masu yawa sun yi kaura zuwa Katsina inda suke tsammanin su sami sakewa.
Wannan dalili na tabarbarewar Musulunci da shugabanci a cikin al'umma a dukkanin kasar Hausa yasa dole akwai bukatar yin Tajdidi wato yin Jihadi. Don haka ne kamar yadda muka yi bayani a Shehu Usman Dan ya fara kaddamar da Jihadi domin kawo gyara.
Lokacin da Shehu Usman Dan Fodio ya fara Jihadi, a nan Kano akwai jinsin Fulani iri daban daban. Ga jerin jinsin Fulani da ke Kano da kuma jagororin su:
- Danejawa karkashin jagorancin Malam Dan Zabuwa
- Mundubawa karkashin jagorancin Malam Sulaimanu
- Sullubawa karkashin jagorancin Malam Jamo
- Yolawa karkashin Malam Jibir
- Jobawa karkashin jagorancin Malam Bakatsine
- Dambazawa karkashin jagorancin Malam Dabon Dambazau
- Yarimawa karkashin jagorancin Malam Dantunku
Wadannan jinsi da sauran su sune Fulanin da suke zaune a Kano tsawon zamani. Kuma lokacin da Shehu Usman Dan Fodio ya fara Jihadi, su suka taru don kaddamar da Jihadi a Kano. A lokacin suka tsayar da Malam Dan Zabuwa a matsayin wanda zai jagoran ce su domin karbo tutar Jihadi a wajen Shehu. Bayan sun karbo tutar Jihadi, sai suka yi sansani a wani wuri da ake kira "Kwazazzabon Yar Kwando". Bayan sun hada karfi guri guda, sai suka ayyana jihadi akan Masarautar Kano. A wannan lokaci kuwa Sarkin Kano Muhammadu Alwali ne yake mulki a matsayin Sarkin Kano. Tashin fari masu jihadi suka cinye Karaye daga nan suka nufo Kano suka sauka a Tudun Fulani. Sarkin Kano Alwali ya fito da rundunar yakin sa, kuma aka gwabza yaki. Sai dai masu jihadi suka ci nasara akan sa. Daga nan Sarki Alwali da wasu dakarun sa suka gudu zuwa Zariya, amma Sarkin Zazzau bai yarda ya taimake shi ba. Alwali ya juyo daga Zariya ya sake shigowa cikin kasar Kano. Bayan shigo kasar Kano, sai yaci Karo da rundunar masu Jihadi a Burum Burum. A garin Burum Burum ne masu Jihadi suka samu nasarar kashe Sarkin Kano Alwali. Wannan kuma ya basu damar karbe mulkin Kano baki daya.
Bayan masu Jihadi sun samu nasarar karbe ikon mulki a Kano, sai suka yi ayari suka tafi gurin Shehu Usman Dan Fodio. Bayan sun je, sai suka bukaci Shehu ya nada Sabon Sarkin Kano. Kamar yadda Wazirin Kano Alhaji Abubakar Dokaji ya kawo a littafin sa mai suna "Kano Ta Dabo Ci Gari" yace Shehu ya tambaye su "waye limamin ku" sai suka ce "Sulaimanu". Don haka Shehu yace "Imamikum Amirukum ", wato "Limamin ku Shugaban Ku". Da wannan dalili ne Shehu Usman Dan Fodio ya nada Sulaimanu dan Abuhama a matsayin sabon Sarkin Kano a shekarar 1807. Kuma hakan ya samar da sabuwar Masarautar Kano bisa shari'ar Musulunci wadda Sarki zai dinga yin hukunci bisa Al'kurani da Sunnah.
0 Comments