![]() |
Sarkin Kano Sulaimanu |
Malam Sulaimanu dan Abuhama ya zama Sarkin Kano a shekarar 1807 bayan da aka tunbuke Sarkin Kano Alwali daga gadon sarautar Kano a lokacin kaddamar da Jihadi. Kuma shi Sarkin Kano Alwali shine Sarkin Kano na karshe a jerin Sarakunan Kano Hausawa.
Sarkin Kano Sulaimanu ya fito ne daga kabilar Fulani "Mundubawa". Kuma ya kasance mutum ne mai ilmi da tsoron Allah. Haka kuma mutum ne mai sanyin hali da tausaya Jama'a. A matsayin sa na Sarkin Kano, ya tattara dukkan yan uwan sa Fulani ya rungume su, ya tafi da su baki daya. Yayi mulki ne a kewaye da mutane musamman wadanda suka yi Jihadi a tare da shi a Kano.
Tarihi ya tabbatar da cewa bayan da aka cinye Kano aka tabbatar wa Malam Sulaimanu da sarauta, sai kowacce kungiya ta Fulani tayi kokari ta kwace mulkin kasar da take zaune a cikin ta daga hannun masu mulkin ta kafin Jihadi. Har an ce wasu daga cikin jagororin Jihadi sun ki bawa Sarki Sulaimanu hadin kai saboda suna ganin su suka fi cancanta da zama Sarkin Kano. Wannan tirka-tirka ta ci gaba har sai da Shehu Usman Dan Fodio yayi musu sulhu, tare da umartar su akan biyayya ga Sarki.
Haka kuma tarihi ya tabbatar da cewa Sarkin Kano Sulaimanu ya jima da zama Sarkin Kano amma bai shiga gidan Sarautar Kano ba. An ce wata rana wani mutum daga jama'ar Habe (Hausawa) ya ce wa Sarki Suleimanu idan har baka shiga gidan Sarki ba, babu shakka baza ka ci galabar Kanawa na cikin gari dana kauye ba. Jin haka sai Sarki ya kirawo taro na sauran shugabannin Fulani da suka yi Jihadi a Kano ya tattauna da su akan al'amarin. Don haka aka yanke shawarar a tuntubi shugaban Musulunci wato Shehu Usman Dan Fodio. Shehu ya amince ya saka albarka. A wannan lokaci Shehu ya bawa Sarkin Kano Sulaimanu takobi da wuka, da tuta, da kundi, da kayan fada irin na mulki. Don haka ne Sarkin Kano Sulaimanu ya shiga gidan Sarautar Kano tare da karfin gwiwa kuma ya ci gaba da harkokin mulki.
Sarkin Kano Sulaimanu yayi shekara goma sha uku (13) yana Sarautar Kano daga shekarar 1807 zuwa shekarar 1819.
0 Comments