TARIHIN SARKIN KANO IBRAHIM DABO

Sarki Ibrahim Dabo 

Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya fito ne daga tsatson kabilar Fulani ta Sullubawa. Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya kasance dan Malam Mamuda dan Abdulmalik dan Modibbo Kwaire. Haka kuma yana cikin wadanda suka taimaka wajen gudanar da Jihadi a Kano. A lokacin sa mulkin Masarautar Kano ya kara kyautatuwa matuka, har ma wasu masana tarihi suna ganin cewa Sarkin Kano Ibrahim Dabo ne Sarki mafi tasiri a Sarakunan Kano bayan Sarkin Kano Muhammadu Rumfa.

Nadin Ibrahim Dabo a matsayin Sarkin Kano 

Kamar yadda Wazirin Kano Alhaji Abubakar Dokaji ya kawo a cikin littafin sa mai suna "Kano Ta Dabo Ci Gari" yace lokacin da ciwon ajali ya kama Sarkin Kano Sulaimanu sai ya aika da takarda yace da Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya zabi wanda yafi dacewa da sarauta. Sai dai an ce shi Sarki Sulaimanu ya bawa Sarkin Musulmi shawara cewa kada ya nada daya daga cikin manyan jagororin Fulani a Kano, saboda idan sun sami mulki zalunci za su yi. Ya kuma bayar da shawara cewa a nada Ibrahim Dabo na kabilar Fulani Sullubawa. A wani bangaren kuma, lokacin da Sarki Sulaimanu ya rasu sai Malam Yunusa Dabon Dambazau shugaban Fulani Dambazawa ya aika wa Sarkin Musulmi Muhammadu Bello cewa yana bukatar sarautar Kano. Sai dai Sarkin Musulmi ya riga ya yanke shawarar nada Malam Ibrahim Dabo a matsayin Sarkin Kano. Don haka aka bawa Dabon Dambazau hakuri tare da yi masa alkawarin idan Dabon Sullubawa ya rasu za'a nada. Wannan dalili ne yasa ake kiran sa da Sarkin Baya, kuma daga wannan ne sunan Sarautar Dambazawa ta Sarkin Bai ta samo asali.

Bayan nan sai Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya aiko da izini domin a nada Ibrahim Dabo a matsayin Sarkin Kano. An ce lokacin ake nada Ibrahim Dabo a cikin Masallaci, sai wani waliyyi da ke zaune a cikin masallacin yace "Wa ake nada wa a matsayin Sarkin Kano" sai aka ce "Dabo dan Mahmudu" sai yace "Wane mutum, kuna yin mubaya'a ga hannun da sarauta baza ta subuce daga gare shi ba". Wannan abu kuma ga shi ya tabbata, domin har yanzu jinin Ibrahim Dabo ne suke Sarautar Kano.

Tawaye a Farkon Mulkin Ibrahim Dabo 

An samu tawaye daga bangarori da dama na kasar Kano a farkon mulkin Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Da yawa daga cikin manyan Dagatai da masu rike da sarauta a Kano sun nuna kin goyon baya ga Ibrahim Dabo, saboda suna ganin baya cikin jagororin Fulani da suka jagoranci Jihadi a Kano. 

Farkon tawaye ya fito ne daga bangaren Galadiman Kano Sani kanin Sarkin Kano Sulaimanu. Tarihi ya tabbatar da cewa shi Galadima Sani abin da yake so shine bayan rasuwar wan sa wato Sarki Sulaimanu, sai a nada shi ya gaje shi. Don haka yanzu tunda bai samu ba, sai ya fito da hanyar tawaye ga sabon Sarkin Kano.

Tawaye na biyu kuma shine tawayen Sarkin Fulanin Arewacin Kano Malam Usman Dan Tunku na Kabilar Fulani Yarimawa. An ce lokacin da Sarki Sulaimanu ya rasu, sai Dan Tunku yace to yanzu shima zai ci gashin kan sa, wato dai Arewacin Kano ya zama karkashin sa a matsayin Sarki. Dalilin yin haka kuwa shine an ce shi Dan Tunku yana cikin jagororin Fulani da suka karbo tutar Jihadi domin kaddamar da Jihadin a kasar Kano. Saboda haka da aka nada Ibrahim Dabo a matsayin Sarkin Kano, sai yace "baza ta sabu ba, ace mu da muka jagoranci Jihadi muna kallo a bawa wanda bai kai mu shan wahala ba".

Haka kuma akwai manyan Dagatai irin su Sarkin Rano, da Sarkin Fulanin Sankara da sauran wasu wanda suma suka yi tawaye. Suka ce baza su bi Sarki Dabo ba, don haka suma gashin kan su za su ci. 

Ana sa bangaren, Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya fada musu cewa suyi biyayya, ko kuma da sannu zai karya su. Don haka ya shiga halwa ta tsawon ta tsawon kwana arba'in a turakar sa. An ce bai fito ba sai da ya samu rauhanai masu yi masa hidima. Bayan fito ya shirya rundunar yaki, kuma ya tunkari yan tawaye a duk fadin Kano ya dinga yakar su har tsawon shekara hudu. Duk garin da ya tunkara sai ya cinye su da yaki. Yakin da yafi daukar lokaci shine rigima da Dan Tunku. Daga karshe Sarkin Kano Dabo ya samu nasara ya kori Dan Tunku da mayakan sa daga cibiyar mulkin su a Dambatta ya rarake shi har zuwa tsallaken kogi. Daga nan ne Sarki Dabo ya dawo, sakamakon Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya shiga tsakani. Kuma a wannan lokaci ne Sarkin Musulmin ya roki Sarkin Kano, da Sarkin Daura, da Sarkin Katsina akan su yiwa Dantunku karo-karon yankin kasar su domin ya kafa Masarautar sa. Haka kuwa aka yi, wannan ne asalin kafuwar Masarautar Kazaure.

Kafuwar Mulkin Dabo 

Bayan da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya samu nasara akan yan tawaye a fadin kasar Kano, sai ya aikewa Sarkin Musulmi Muhammadu Bello yace yana son yayi masa izini ya dauki wasu daga cikin al'adun sarauta na Sarakunan Habe wato Hausawa. Ya bayyana wa Sarkin Musulmi cewa idan ba haka aka yi ba, addini da shari'a baza su yi karfi ba. Don haka Sarkin Musulmi yayi na'am da wannan shawara kuma yayi masa izini amfani da al'adun. 

Da farko Sarki Dabo ya fara nada sarautu na tun lokacin habe domin kafa Majalisar Sarki masu bayar da shawara da kuma Majalisar masu zaben Sarki.

Da farko ga sarautun da suke na Yan Majalisar Sarki masu bashi shawara: 

  1. Galadima
  2. Wamban 
  3. Sarkin Dawakin Tsakar Gida 
  4. Ciroma 
  5. Turaki 

Bayan wadannan yan Majalisa masu bawa Sarki shawara. Ga kuma sarautun masu zaben Sarki wanda su ma yan Majalisar Sarki ne masu bashi shawara:

  1. Sarautar Madakin Kano ya bawa kabilar Fulani Yolawa 
  2. Sarautar Makaman Kano ya bawa kabilar Fulani Jobawa 
  3. Sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta ya bawa kabilar Fulani Sullubawa na gidan Malam Jamo
  4. Sarautar Sarkin Bai ya bawa kabilar Fulani Dambazawa 
  5. Sarautar Dan Iya ya bawa kabilar Fulani Danejawa na gidan Malam Dan Zabuwa 
  6. Sarautar Mai Unguwar Mundubawa ya bawa kabilar Fulani Mundubawa zuriyar Sarkin Kano Sulaiman

Saboda haka da wadannan Sarautu Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya fara tabbatar da ikon Masarautar Kano. Haka kuma bayan wadannan sarautun hakimai, sai Sarkin Kano Dabo ya nada sarautun manyan bayi masu yiwa Sarki hidima kamar haka :

  1. Shamaki : shugaban bayi ga baki daya
  2. Dan Rimi : mai kula da hakimai da sauran hidimomin Sarki na waje
  3. Sallama: mai yiwa duk mai son ganin Sarki iso
  4. Kasheka: mai kula da wasu larurorin Sarki 
  5. Turakin Soro : mai kula da fitar Sarki zuwa fada ko shigar sa zuwa cikin gida 
  6.  Kilishi: mai kula da shimfidar Sarki
  7. Sarkin Hatsi: shine mai kula da dukkan kayan 
  8. Sarkin Dogari: mai kula da tsaron lafiyar Sarki 
  9.  Jakadan Garko: shine Jakadan Sarki a garin Garko
  10.  Galadiman Fanisau: shine Jakadan Sarki a garin Fanisau 

Izzar Sarauta 

Haka kuma Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya inganta wasu al"adu wanda suka kebanta ga Masarautar Kano. Wadannan al'adun sun hada da:

  1. Saka takalmi mai gashin jimina 
  2.  Kewaye Sarki da fadawa suke yi a lokacin da Sarki zai zauna ko zai tashi 3
  3. Rike Tagwayen Masu wanda Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya fara yin
  4. Sarkin Kano Ibrahim Dabo ne ya fito da al'adar yin nada mai kunne biyu 
  5. Sarkin Kano Ibrahim Dabo ne ya fito da al'adar hakimai su zauna akan dabe, shi kuma yana karaga 

Wadannan aikace-aikace da Sarkin Kano Ibrahim Dabo yayi domin inganta ikon Masarautar Kano, shine ya taimaka wajen kiyaye alfarma da mutuncin sarauta da tsayar doka a duk fadin kasar Kano. Kuma haka ya kara bawa Kano damar rike kambu na zama Masarauta mafi tasiri a duk fadin kasar Hausa ko Daular Usmaniyya.

Iyalan Sarkin Kano Dabo

Sarkin Kano yana da mata wadda ake kira da suna 'Shekara'. Sarki Dabo ya haifi ya ya biyar matar sa Shekara. Wadannan sune kamar haka:

  1. Usman wanda yayi Sarkin Kano daga shekarar 1846 zuwa 1855
  2. Abdullahi wanda yayi Sarkin Kano daga shekarar 1855 zuwa 18823
  3. Muhammadu Bello wanda yayi Sarkin Kano daga shekarar 1882 zuwa 1893
  4. Abdussalam  
  5. Hassan 

An ce Sarki Dabo ya saka wa babban dan sa suna Usman saboda neman tubarrakin Shehu Usman Dan Fodio. Ya sakawa dan sa na biyu Abdullahi saboda neman tubarrakin Abdullahi kanin Shehu Usman. Haka kuma ya sakawa dan sa na uku suna Muhammad Bello saboda neman tubarrakin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dan Shehu Usman Dan Fodio.

Har zuwa yau, tsatson Sarkin Kano Ibrahim Dabo ne suke mulkin Sarautar Kano.

Rasuwar Sarkin Kano Ibrahim Dabo 

Sarki Dabo ya shekara ashirin da bakwai yana Sarkin Kano kafin ya rasu. An ce lokacin da Sarki Dabo ya rasu, wata aljana tayi kuka har sai da kowa yaji a gidan Sarki gabas da yamma, kudu da arewa. Ita wannan aljana ance wai ita ce tayi kuka lokacin da Sarkin Kano Abbas ya rasu.

Bayan rasuwar Sarkin Kano Ibrahim Dabo ba ayi wani kace-nace ba sai Sarkin Musulmi ya nada babban dan sa wato Usman a matsayin sabon Sarkin Kano.



Post a Comment

0 Comments

Close Menu