SARAKUNAN KANO FULANI

Kofar Fadar Masarautar Kano da kuma Hatimin Masarautar Kano 

Fulani sun fara mulkin Kano ne bayan da aka kaddamar da Jihadi Kano a cikin shekarar 1807. Shi kuma Jihadin Kano ya samo asali ne daga Jihadin da Shehu Usman Dan Fodio ya kaddamar a yankin kasar Gobir. Wannan dalili yasa sauran kasashen Hausa ciki har da Kano suka kaddamar da nasu Jihadin na kawar da azzaluman shugabanni da tabbatar da Shari'ar Musulunci.

Tun daga shekarar 1807 zuwa yau shekarar 2024, an yi Sarakunan Kano wanda suke jinin Fulani har guda goma sha biyar (15). Ga jerin su kamar haka:


1. Sarkin Kano Sulaimanu (1807-1819)

2. Sarkin Kano Ibrahim Dabo (1819-1846)

3. Sarkin Kano Usman Maje-Ringim (1846-1855)

4. Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi (1855-1882)

5. Sarkin Kano Muhammadu Bello (1882-1893

6. Sarkin Kano Muhammadu Tukur (1893-1894)

7. Sarkin Kano Alu Mai Sango (1894-1903)

8. Sarkin Kano Abbas Maje-Nasarawa (1903-1919)

9. Sarkin Kano Usman Dan Tsoho (1919-1926)

10. Sarkin Kano Abdullahi Bayero (1926-1953)

11. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I (1953-1963)

12. Sarkin Kano Muhammadu Inuwa (1963-1963)

13. Sarkin Kano Ado Bayero (1963-2014)

14. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II (2014-2020, 2024 zuwa yau)

15. Sarkin Kano Aminu Ado Bayero (2020-2024)


Wadannan sarakuna sune suka mulki Masarautar Kano daga 1807 har zuwa yau.

111

Post a Comment

0 Comments

Close Menu