TARIHIN YAKE-YAKEN SARKIN KANO IBRAHIM DABO

Sarkin Kano Ibrahim Dabo da mayakan sa

Kamar yadda muka fada muku a baya cewa lokacin da aka nada Sarkin Kano Ibrahim Dabo, an samu tawaye a sassa daban-daban a kasar Kano. Wasu daga cikin garuruwan dake karkashin Masarautar Kano sun yi tawaye sun ce baza su bi Sarki Dabo ba. Don haka shi kuma Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya dauki aniyar yakar duk wani wanda yayi masa tawaye. Wannan dalili ne yasa Sarkin Kano Dabo yayi wasu yake-yake har na tsawon shekara bakwai kafin ya murkushe tawaye a fadin kasar Kano daga shekarar 1819 zuwa 1826.

Bari mu duba wasu daga cikin Yake-yaken da Sarkin Kano Ibrahim Dabo yayi domin murkushe yan tawaye.

Yakin Sankara 

Daya daga cikin wanda suka yiwa Sarkin Kano Ibrahim Dabo tawaye akwai Sarkin Fulanin Sankara wato Ardo Hunturbe. Don haka ne Sarki Dabo ya shirya rundunar yaki domin yakar Sankara. Amma kafin Sarkin Kano Dabo ya iso Sankara, tuni Ardo Hunturbe ya samu labarin cewa Sarki ya taho domin ya murkushe Sankara. Don haka ne Ardo Hunturbe ya tara mayakan sa domin tunkarar Sarkin Kano. Hunturbe ya raba mayakan sa kashi na biyu. Kashi na farko shine kungiyar maharba wadanda shi Ardo Hunturbe yake jagoranta. Kashi na biyu kuma sune kungiyar barada da dakaru wadanda Tunare dan Sarkin Fulanin Sankara yake yi wa jagora. 

A nasa bangaren, da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya samu labarin shirin da Sarkin Fulanin Sankara yayi na yaki, shima sai yayi irin wannan shirin yace "tunda fadan Ardo da kibiya za'a yi, to ai kuwa ya bamu aikin da zamu iya." Sarki Dabo ya raba mayakan sa kashi biyu. Kashi na farko Barade masu dawaki yasa Jarmai Sulaimanu wanda ake yi wa kirari da "Garkuwar Karfe". Kashi na biyu kuma sai shi Dabo ya jagorance su da kan sa. 

To da wannan shiri ne Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya malalo da mayakan sa zuwa Sankara. Da zuwan sa kuwa yaki ya fara tsakanin mayakan Sarki Dabo da mayakan Ardo Hunturbe. Haka aka dinga gwabza yaki har mutanen Sankara suka juya suka gudu. Sarkin Kano Dabo ya bisu ya samu Ardo Hunturbe aka harbe shi da kibau ya fado daga kan dokin sa ya mutu. Haka dai Sarkin Kano Ibrahim Dabo da mayakan sa suka tausa kora, suka tarwatsa sauran mayakan Ardo Hunturbe har zuwa iyakar kasar Kano da Daura. Sarki Dabo ya kone garin Sankara ya rushe ganuwar garin.

Yakin Rano

Bayan da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya murkushe tawayen Sankara, sai duk sauran yan tawaye a kasar Kano suka firgita. Shi kuma Dabo da ya ga lallai abokan gabar sa sun firgita sai kawai ya kara kaimin dawakan yakin sa, ya yi wa makiyan nasa 'Furji daf da kamu ' wato ya kara razana su da hallaka. Don haka daga nan Sarki Dabo ya daura shirin yakin Rano.

Kafin Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya nufi Rano domin yakar tawayen su, ya tara mayakan sa inda yayi musu huduba game da yakin da suka yi saboda kashe fitinar tawaye da wargajewar jama'a (anarchy). Don haka daga nan ya sanar da su cewa yanzu za'a tunkari Rano.

A Rano Barwan Rano ya fito da yaki ba na wasa ba ya tunkari rundunar Sarkin Kano Dabo, aka gwabza yaki a bakin tafkin Rano tun safe har wajen la'asar sannan Allah ya bawa Sarkin Kano Dabo da mayakan sa nasara suka ci galaba akan rundunar mayakan Rano karkashin jagorancin Barwan Rano. A wannan lokaci an kashe Barwan Rano da wasu daga cikin hadiman sa, don haka sauran mayakan sa suka gudu, wasu kuma suka shiga cikin garin Rano. Amma Sarkin Kano Dabo ya bi su har zuwa cikin garin Rano ya zauna, aka yi masa aski kuma tun daga wannan lokaci Sarki Dabo baya aski sai yaci gari. Bayan Sarkin Kano Dabo ya kammala murkushe yan tawayen Rano, sai ya nada sabon Sarkin Rano daga kabilar Fulanin garin wadanda suka taimaka a wajen yakin. Sabon Sarkin Rano da aka nada shine Isau, wanda kuma har yanzu zuriyar sa ne suke rike sarautar Rano.

Yakin Dantunku 

Bayan da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya dawo daga Yakin Rano, sai wani mutum (watakila daga kungiyar Yarimawan Danbatta) ya aiko masa labarin cewa Dambo babban dan Dantunku yana nan a Kunci shi da rabin mayakan mahaifin sa wato Dantunku. Mai bada wannan asirin kuwa shine Galadima Hadiri dan Gebi. Shi kuma Gebi ya kasance wa ga Dantunku.

Da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya gama samun labarin yadda Dambo da mayakan sa suka yi sansani a Kunci, sai kawai Sarki yayi murna yace "Alhamdu Lillahi" yakin Dantunku ya karye ". Sarki ya hada mayaka masu yawa ya nada Sarkin Yakin Kano Aliyu ya jagoranci wannan runduna zuwa Kunci domin yakar Dambo dan Dantunku. Sarkin Yaki Aliyu yaja mayakan sa zuwa Kunci, ya keci jeji dan kada labari ya kaiwa Dambo akan tahowar sa. Har Sarkin Yaki ya isa Kunci cikin tsakiyar dare ba wanda ya san ya iso garin. Bayan da mayakan sa suka huta kadan, da asubar fari suka afkawa mayakan Dambo yaki. Sarkin Yaki da mayakan sa sun kewaye Kunci, sun saka mata wuta. Suka yi kaca-kaca da garin Kunci, suka karkashe mayakan Dambo, amma duk da haka sai da Dambon ya kubuta, ya sulale ya gudu wajen uban sa Dantunku. Da gari ya waye Sarkin Yaki Aliyu ya ci gaba da murkushe kauyukan da suke kusa da Kunci, har suka lashe su gaba daya. Bayan ya cinye yan tawayen, sai ya dawo cikin nasara da ganima ya tarar da Sarkin Kano Ibrahim Dabo a Tattarawa yana dakon sa. Yana iso Sarkin Yaki Aliyu ya fadi kasa ya gaida Sarkin Kano Dabo, kuma ya bashi labarin irin yadda ya yaki Dambo a garin Kunci da shauran kauyukan da suka kewaye ta. Da Sarki yaji wannan labari, sai yayi farin ciki ya godewa Sarkin Yaki Aliyu kuma yace yaje ya huta a masaukin sa kafin a sake bashi umarni na gaba.

Bayan da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya samu nasarar kwace mafi yawancin garuruwan da Dantunku ya kame a kasar Kano, kuma aka kore shi yayi Arewa, sai Sarki ya zauna a Fanisau kamar shekara guda yana shirin bin Dantunku ya yake shi duk inda ya same shi. Sarki ya aikawa yan uwan sa Sarakuna da neman taimako akan abin da yayi niyya, sarakuna suka aiko masa da taimako mai yawa na dawaki da kayan yaki. Bayan nan, Sarkin Kano Dabo yasa aka kada kugen yaki da safe, ya kuma umarci Kanawa da a tafi a Kamo Dantunku a hannu. Sarki Dabo ya fito yakin Dantunku daga Fanisau, kuma tunda ya fito kura ta murtuke gabas da yamma, kudu da Arewa ba mai ganin ko da tafin hannun sa saboda tsananin kurar yaki.

Da Dantunku ya samu labarin fitowar rundunar Sarkin Kano Ibrahim Dabo zuwa gare shi, sai yayi tsammani abin na wasa ne, wato sai yayi zaton irin yake-yaken da ya gani ne wanda yayi da mutanen Dabo a shekarun da suka wuce. Don haka shima sai ya hada kan mayakan sa ya nufo Sarkin Kano Dabo. Dantunku yayi rashin sa'a ya hadu da rundunar Sarkin Kano a wata yar korama wacca ake kira Sabon Ruwa bayan an ketare Tomar kadan. Koda mayakan Sarkin Kano Ibrahim Dabo suka yi arba da Dantunku da mayakan sa, sai kawai suka yi cida, suka rude da kururuwa suka fada Dantunku da yaki. Nan kura ta murtuke tayi sama ta rufe sararin samaniya. Rana ta zama kamar dare saboda kura. Bayab wani lokaci, tuni mayakan Sarkin Kano sun ci galaba akan mayakan Dantunku, don haka Dantunkun da jama'ar suka danna a guje domin tsira da ran su. Da Dantunku ya gudu sai Sarki Dabo yace shi don kada ya tsira. Don haka Sarkin Kano da mayakan sa suka bi Dantunku. Sarki ya bi Dantunku zuwa Dambatta, amma sai ya tarar tuni Dantunku ya kwashe komai nasa ya gudu Arewa. Aka bishi har ketaren Kurungufi, yayi sansani tsakanin Kurungufi da Kazaure. Sai ya aikawa da dan uwan sa Dambon Ingawa yana sanar da shi cikin halin da yake ciki. Sai Dambo ya taho da mayakan sa na Katsinawa suka bullowa Kanawa ta yamma. Suka yi sa'a suka hadu da masu karagar Sarkin suka yi fada da su har suka kwace karagar Sarkin Kano. Rundunar Sarkin Kanawa da suka ga haka sai suka ja da baya suka ketare Kurungufi dan kada a kewaye su. Wannan karaga ita ce ta zama alatun sarauta a Kazaure, kuma har yanzu tana nan a garin Kazaure. Daga nan sai Dantunku ya tashi nufin sa ya tafi Daura daga nan. Zai wuce babban Dutse, sai wani bamaguje ya fito daga gindin dutse ya kwala kira yace; "Kai Danfulani ! Kai Danfulani ! !. Da mutane suka ji haka sai suka shaidawa Dantunku shi kuma sai ya dakata har Bamagujen yazo kusa da shi. Yace da Dantunku "Uban na ya bar min wasiyya da zai mutu, yace kada ka wuce nan. Mu zauna da kai nan ne wurin arzikin ka." Dantunku ya sauka daga kan dokin sa ya bi shawarar Bamaguje, ya kafa bukkoki da shi da iyalan sa da mabiyan sa gindin dutsen nan. Shi wannan bamaguje sunan sa Kazaure. Bayan Dantunku ya huta na wadan su kwanaki, sai ya kira babban dan sa Dambo ya bashi takarda ya tura shi Sokoto wajen Sarkin Musulmi Muhammadu Bello cewar ga abin da ya faru tsakanin sa da Sarkin Kano. Sai Sarkin Musulmi Bello yace kararrakin da rigimar Dantunku sun yi yawa, amma duk da haka an yafe masa. Bello yasa aka rubuta takarda ya kuma hada su da Galadiman Sokoto, ya umarci Sarkin Kano, da Sarkin Katsina, da kuma Sarkin Daura akan su yiwa Dantunku ayagar kasa daga cikin yankin su don ya zama Sarki mai tuta kamar kowanne Sarki. Don haka ne wadannan Sarakuna suka bi umarnin Sarkin Musulmi. Hakan kuma shine asalin kafuwar Masarautar Kazaure.

Da Dambo ya dawo ya samu cewa mahaifin sa Dantunku ya tashi yin sallah sai ya taka kunamar bindiga a daki wuta ta tashi amma Dantunku yaki fitowa daga dakin, dan kunya da jarumtaka har wutar ta kona shi ya zama ajalin sa. Saboda haka Dambo ya zama Sarkin Kazaure na farko. An debi wani yanki na kasar Daura daga Arewa, an debi wani yanki na kasar Katsina daga yamma, an debi wani yanki na kasar Kano daga gabas da kudu da Kazaure aka hada aka ce nan ce ikon Masarautar Kazaure karkashin Dambo. Kuma an taru an gina Kazaure, an tabbatarwa Dambo kasar sa an sashi daga cikin Sarakunan yanka an yi masa uban daki da Galadiman Sokoto.


Tushen Bayani (Reference)

Muhammad Uba Adamu, (2007), Kano Da Makwabtan ta"

Post a Comment

0 Comments

Close Menu