Mayakan Sarkin Kano |
Kamar yadda muka fada muku a baya, lokacin da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya zama Sarki, yayi fama da rigimar tawaye daga sassa daban-daban na kasar Kano.
Daya daga cikin wanda suka yiwa Sarkin Kano Ibrahim Dabo tawaye akwai Sarkin Fulanin Sankara wato Ardo Hunturbe. Don haka ne Sarki Dabo ya shirya rundunar yaki domin yakar Sankara. Amma kafin Sarkin Kano Dabo ya iso Sankara, tuni Ardo Hunturbe ya samu labarin cewa Sarki ya taho domin ya murkushe Sankara. Don haka ne Ardo Hunturbe ya tara mayakan sa domin tunkarar Sarkin Kano. Hunturbe ya raba mayakan sa kashi na biyu. Kashi na farko shine kungiyar maharba wadanda shi Ardo Hunturbe yake jagoranta. Kashi na biyu kuma sune kungiyar barada da dakaru wadanda Tunare dan Sarkin Fulanin Sankara yake yi wa jagora.
A nasa bangaren, da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya samu labarin shirin da Sarkin Fulanin Sankara yayi na yaki, shima sai yayi irin wannan shirin yace "tunda fadan Ardo da kibiya za'a yi, to ai kuwa ya bamu aikin da zamu iya." Sarki Dabo ya raba mayakan sa kashi biyu. Kashi na farko Barade masu dawaki yasa Jarmai Sulaimanu wanda ake yi wa kirari da "Garkuwar Karfe". Kashi na biyu kuma sai shi Dabo ya jagorance su da kan sa.
To da wannan shiri ne Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya malalo da mayakan sa zuwa Sankara. Da zuwan sa kuwa yaki ya fara tsakanin mayakan Sarki Dabo da mayakan Ardo Hunturbe. Haka aka dinga gwabza yaki har mutanen Sankara suka juya suka gudu. Sarkin Kano Dabo ya bisu ya samu Ardo Hunturbe aka harbe shi da kibau ya fado daga kan dokin sa ya mutu. Haka dai Sarkin Kano Ibrahim Dabo da mayakan sa suka tausa kora, suka tarwatsa sauran mayakan Ardo Hunturbe har zuwa iyakar kasar Kano da Daura. Sarki Dabo ya kone garin Sankara ya rushe ganuwar garin. Ya kuma jaddada ikon Masarautar Kano akan Sankara.
0 Comments