YAKIN RANO

Yakin Rano

Yakin Rano Yana daya daga cikin yake-yaken da Sarkin Kano Dabo ya yi a kokarin sa na murkushe yan tawaye a kasar Kano. Lokacin da Ibrahim Dabo ya zama Sarki, Rano tayi tawaye don haka Sarkin Kano ya shirya yakar ta. Don haka za mu yi bayanin yadda yakin ya kasance.

Bayan da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya murkushe tawayen Sankara, sai duk sauran yan tawaye a kasar Kano suka firgita. Shi kuma Dabo da ya ga lallai abokan gabar sa sun firgita sai kawai ya kara kaimin dawakan yakin sa, ya yi wa makiyan nasa 'Furji daf da kamu ' wato ya kara razana su da hallaka. Don haka daga nan Sarki Dabo ya daura shirin yakin Rano.

Kafin Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya nufi Rano domin yakar tawayen su, ya tara mayakan sa inda yayi musu huduba game da yakin da suka yi saboda kashe fitinar tawaye da wargajewar jama'a (anarchy). Don haka daga nan ya sanar da su cewa yanzu za'a tunkari Rano.

A Rano Barwan Rano ya fito da yaki ba na wasa ba ya tunkari rundunar Sarkin Kano Dabo, aka gwabza yaki a bakin tafkin Rano tun safe har wajen la'asar sannan Allah ya bawa Sarkin Kano Dabo da mayakan sa nasara suka ci galaba akan rundunar mayakan Rano karkashin jagorancin Barwan Rano. A wannan lokaci an kashe Barwan Rano da wasu daga cikin hadiman sa, don haka sauran mayakan sa suka gudu, wasu kuma suka shiga cikin garin Rano. Amma Sarkin Kano Dabo ya bi su har zuwa cikin garin Rano ya zauna, aka yi masa aski kuma tun daga wannan lokaci Sarki Dabo baya aski sai yaci gari. Bayan Sarkin Kano Dabo ya kammala murkushe yan tawayen Rano, sai ya nada sabon Sarkin Rano daga kabilar Fulanin garin wadanda suka taimaka a wajen yakin. Sabon Sarkin Rano da aka nada shine Isau, wanda kuma har yanzu zuriyar sa ne suke rike sarautar Rano.


Tushen Bayani (Reference)

Muhammad Uba Adamu, (2007), "Kano Da Makwabtan ta"

Post a Comment

0 Comments

Close Menu