TARIHIN FULANI A KASAR HAUSA

Fulani 


Gabatarwa

Kasar Hausa ta sami shigowar kabilu iri-iri daga nihiyoyin duniya daban-daban musamman daga manyan daulolin Africa ta Yamma. Misali, Kasar Kano wadda ta kasance babbar cibiyar Kasar Hausa ta ga hada-hadar shigowar baki daban-daban a cikin kungiyoyi tun daga wajejen karni na tara wato "9th century" a turance.

Babbar kabilar data shigo cikin kasar Hausa kuma ta samu gindin zama fiye da kowacce kabila ita ce 'Kabilar Fulani ". Hakika kungiyoyin Fulani sun yi hijra zuwa kasar Hausa inda suka barbazu a cikin garuruwa da kauyuka har suka sami kafa mazaunai. Misali, zaka samu Fulani ne suka kafa da yawa daga cikin wasu garuruwan kasar Hausa 

Asalin Fulani da Shigowar su Kasar Hausa 

Masana tarihi da yawa sun tabbatar da cewa asalin Fulani sun fito ne daga cikin Larabawa. Masanan sun bayar da misali cewa Fulani da Larabawa suna kamanceceniya ta fannin surar jiki da al'adun su. Misali, babbar sana'ar Larabawa ita ce kiwo da noma, haka su ma Fulani.

Masanan sun kara da cewa Fulani sun shigo yankin Africa ta Yamma wato ketaren Kasashen Larabawa daga wajejen kasar Masar daidai gabar Kogin Nilu tun a wajejen karni na bakwi wato "7th Century" a turance. Daga nan suka barbazu yankunan Kasashen Africa ta Yamma musamman Yankin Duwatsun Futa Toro da Futa Djallon dake Senegal a yanzu. Daga nan ne kuma Fulanin a cikin karni na 13th (7th Century) suka taho Kasar Hausa inda suka zauna.

Kabilun Fulani 

Fulani mutane ne masu yawo wadanda suka zagaya sassan Africa da dama. Haka kuma mutane ne masu halaye da al'adun da suka dace da yanayin rayuwar su. Kamar yadda Abdullahi Nasidi Umaru ya kawo a cikin littafin sa mai suna "Daular Fulani a Kano" ya bayyana cewa Fulanin da suka shigo kasar Hausa jinsi daya ne, sai dai sun kasu kashi biyu. Akwai Fulanin Gida da akwai kuma Fulanin Daji.

Su Fulanin Gida wanda ake yiwa lakabi da "Fulanin Soro" mafi yawancin su dogaye ne, wankan tarwada, kuma akan samu farare da bakake a cikin su. Sannan suna da kyawawan idanu da dogayen yatsun hannu dana kafa. Yawancin su makaranta Al'Qurani da litattafan koyar da addinin Musulunci ne kamar Tauhidi da Ibada. Sana'ar su kiwo na cikin gida noma. Halayen su kuwa sun hada da kunya da hakuri da iya jagorancin mutane.

Bafulatanin Gida


Su kuma Fulanin Daji wanda ake yiwa lakabi da "Bororoji" sun kasance jinsin Fulani masu yawo daga wannan guri zuwa wancan guri. Yawancin su farare ne fat kuma kyawawan gaske kamar Larabawa. Wasu kuma wankan tarwada ne, amma akan samu bakake a cikin su. Suna da yawan gashi mazan su da matan su. Fulanin Daji sun kasance masu halin wauta da jarumtaka, gasu kuma da karfin hali da juriya. Sana'ar su kiwon dabbobi daga wannan guri zuwa wancan guri. Sukan zagaya zuwa yankunan da ake samun ciyawa musamman a lokacin rani.

Bafulatanin Daji


Fulanin Daji masu kiwon shanu

Kammalawa 

A takaice dai Fulani ba baki bane a Yankin Kasar Hausa. Sun kwashe fiye da shekaru dari bakwai. Don haka ne suka samu karbuwa a cikin kasar Hausa wadda ta janyo auratayya, kuma hakan ya samar da kalmar "Hausa-Fulani".

Post a Comment

0 Comments

Close Menu