KAFUWAR BIRNIN KANO

Birnin Kano daga kan Dutsen Dala. Source:creativecommons.org

Mazauna Farko a Kano

Kano wani tsohon gari ne wanda ba'a iya tantance ko kiyaye lokacin da aka fara zama a cikin sa ba. Sai dai kuma akwai kauli biyu akan mutanen da suka fara zama a Kano.

Kamar yadda Wazirin Kano Alhaji Abubakar Dokaji ya kawo a cikin littafin sa mai suna "Kano Ta Dabo Ci Gari", yace a wajejen karshen karni na tara wato 9th century a turance, wadansu maharba wadanda ake ganin daga Arewa suke sun zo sun zauna akan duwatsun dake kewaye da sararin da ake kira Kano a yanzu. Irin duwatsun nan sune irin su Dala, Gwauron Dutse, Magwan, da Dutsen Fanisau.

Su Maharban nan suka rika yin farauta a wani kurmi wanda yake shine tushen rafin Jakara, inda Kasuwar Kurmi ta samo suna. Da wadannan maharba suka gwada yin noma suka ga kasar tana da albarka, sai suka ci gaba da saran daji suna yin gonaki. Albarkar kasar Kano ta jawo mutane daga wasu guraren. Da taron mutanen ya fara yawa, sai suka yi shugaba wanda a bisa al'ada ya kasance mafi karfin jiki da karfin tsafi. Babu tahakikanin akan irin tsarin mulkin da wadannan al'umma suka gina shugabancin su. Amma duk da haka ana iya cewa aikin shugaba a wannan lokacin bai wuce tsare dokokin farauta da kuma kusaci da tsafin da mutanen ke bautawa ba. Kuma tarihi ya tabbatar da cewa mazauna farko a Kano suna bautar "Dodon Tsumburbura". Tsumburbura wani dodon tsafi ne wanda ake bautawa, kuma ake yiwa yanke-yanke a duk shekara don ya kusantar da su ga bukatun su na rayuwa. Akan yi wannan yanke-yanke ne a duk farkon shekara inda mutane zasu hadu a gindin Dutsen Dala ana kade-kade da raye-raye, zuwa can sai Barbushe ya fito ya bayyana wa mutane halin za'a shiga a wannan shekara mai kamawa.

Hoton Dutsen Dala. Source:creativecommons.org

Barbushe ne shugaba wanda tarihi ya iya tabbatarwa a jerin shugabanni na mazauna farko a Kano. Sai dai akwai wasu shugabannin da aka yi kafin sa. Shi dai Barbushe ya kasance mutum ne mai karfi da kwarjini wanda saboda karfin sa ance yana kashe giwa ya dora ta a kafada shi kadai yayi tafiya mai nisa da ita har ya kawo ta gida. Gidan Barbushe akan dutsen Dala yake. Shine mai kula da jama'ar dake bautar Gunkin Tsumburbura a duk fadin Kano. Wannan aiki yafi karfin mutum daya wanda yasa Barbushe ya sami mataimaka (Fadawa) wadanda aka dora musu alhakin kula da yankunan da jama'ar dake bautar wannan gunki suka fito. Wadannan Mataimaka na Barbushe sune kamar haka:

  • (1) Dambiru mai kula da jama'ar Dutsen Jigirya 
  • (2) Jandamisa mai kula da Jama'ar Dutsen Magwan 
  • (3) Tanzagu mai kula da jama'ar Dutsen Gwauron Dutse 
  • (4) Hambarau mai kula da Dutsen Tanagar 
  • (5) Gumbarjadu mai kula da Dutsen Fanisau 

Lokacin da Barbushe yayi karfi sosai a cikin harkokin mulki da bauta sai zamanto ya daina fita yawon farauta, inda har takai baya saukowa daga kan Dutsen Dala inda gidan sa yake daga shekara sai shekara domin ya gabatar da jawabin shekara na abubuwan da zasu faru.

Kammalawa 

Da haka wannan gari na Kano ya fara kafuwa, mutane suka fara zama don ci gaban kan su. Wannan ya bada dama ga sauran mutane daga wasu yankunan suka fara yin kaura zuwa Kano.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu