![]() |
Kofar Fadar Sarkin Kano (Gidan Rumfa) |
Kamar yadda Kundin Tarihin Kano wato "Kano Chronicle" ya tabbatar, an ce bayan da Barbushe ya mutu an samu shugabanni da suka biyo bayan sa a yankin Kano. To amma sai aka dinga samun rigingimu na tasowa tsakanin mazauna Kano. Danne hakkin marasa karfi da cin zali suka zama ruwan dare. Babu babba babu yaro, kowa yana cikin damuwa akan lalacewar zamantakewa. Shugabanci ya lalace, ba'a jin tsawatawar shugabanni. Ana cikin wannan hali ne sai a shekarar 999 Miladiyya (999 A.D.) aka samu shigowar wasu dakarun mayaka karkashin jagorancin wani mai suna Bagauda wanda yazo ya kafa sabon mulki a Kano. Shi wannan Bagauda ya kasance dan Bawo Sarkin Daura. Dalilin zuwan Bagauda Kano ta samu tsarin mulki cikakke wanda ya sanya aka samu Masarautar Kano a shekarar 999 A.D. Lokacin da Bagauda zai zo Kano ya taho da wadansu fadawan sa da suka hada da Kududdufi, Buram, Isa, Akasan, Darman, da Goriba. Don haka bayan Masarautar Kano ta kafu, sai aka nada wadannan mutane a matsayin hakimai. Misali, daga sunayen su ne aka samu sarautun hakimai a Kano irin su Dan Buram, Dan Isa, Dan Darman, Dan Goriba, da sauran su.
Kafuwar Mulkin Bagauda a matsayin Sarkin Kano na farko wanda ya samar da nagartaccen tsarin mulki, za'a iya bayyana shi da cewa yayi tasiri wajen gudanar da harkokin mulki a fadin Kasar Kano karkashin tsarin shugabanci guda daya wato "Sarki". Sarki shugaba guda daya ne wanda kowa yake karbar umarni daga gurin sa. Duk fadin kasar Kano tasa ce, shi yake da ikon bayar da ita.
Zuwan Bagauda kuma ya kara bayar da damar bunkasar Kano inda aka samu unguwanni daban-daban domin zaman jama'a. Akwai daga cikin unguwannin da suka samu a wannan lokacin da suka hada da Yakasai, Kankarofi, Sheshe, Gwangwazo, da sauran su.
Ikon Kano Masarautar Kano ya ci gaba da fadada ya zuwa wasu garuruwa dake kusa da Kano irin su Rano, Gaya, Karaye, Dutse, Birnin Kudu, da sauran su. Hakika bunkasar birnin Kano da fadadar mulkin Masarautar Kano dole ya jawo karfin ikon Kano a duk fadin kasar Hausa.
Kammalawa
A takaice dai zamu iya cewa Masarautar Kano ta kafu ne tun a shekarar 999 A.D. Kuma Sarkin Kano na farko shine Bagauda da Bawo. Kuma tun daga wannan lokaci Kano take a matsayin Masarauta.
0 Comments