BUNKASAR BIRNIN KANO


Tsohon birnin Kano

Bayan da mulkin Masarautar Kano ya samu kafuwa, sai daya daga cikin Sarakunan Kano wanda suka yi mulki bayan Bagauda wato Sarkin Kano Gijimasu ya fito da fasahar ginin ganuwar Kano domin bawa birnin Kano kariya daga harin yaki. An fara ginin daga gurin da ake kira Rariya (tsakanin Kofar Dan Agundi da Kofar Na'isa a yanzu) aka yi yamma zuwa Kofar Adama har zuwa wajejen Kofar Kansakali a yanzu. 

Lokacin da yake-yake suka fara yawaita, sai aka dinga haka Kududdufai daf da ganuwa. Dalilin yin haka kuwa don hana abokan gaba shiga gari.

Ganuwar birnin Kano


Abin sha'awa akwai wata waka da yara suke yi inda suke lissafa kofofin Kano kamar haka: Da Kansakali, da Kabuga, Gadon Kaya, Dukawuya, Adama, Kofar Ruwa, Mazugal, Wamban kano.

Kofar Gadon Kaya a shekarar 1903

Shigowar Baki

Bayan da birnin Kano ya sami kariya bisa kyakkyawan tsarin Masarauta, sai aka sami shigowar kungiyoyin mutane daga wurare daban-daban suna zuwa suna zaunawa a lokuta mabanbanta. Misali, a cikin karni na sha uku wato 13th century a turance, an samu shigowar Fulani a rukunonin su mabanbanta kamar Bororoji, Sullubawa , Torankawa, Wangarawa, da sauran su.

Bayan mazaunan farko Hausawa da Fulani wadanda suka shigo tare da kafa mazaunai a Kano, an samu wasu karin bakin da suka shigo zuwa Kano. Akwai Larabawa da suka shigo Kano a sakamakon cinikayya tsakanin kasar Hausa da yankin Arewacin Africa wato "Trabs-Saharan Trade". Amma wasu Larabawan kuma sun zo ne saboda yada addinin Musulunci cikin kungiyoyi karkashin jagorancin shaihunan malamai irin su Muhammadu Abdulkarim Al-Maghili da saurans su.

Shigowar Larabawa yan kasuwa daga Africa ta Arewa ya kara bunkasa birnin musamman ta fuskar ciniki. Wadannan yan kasuwa sun shigo domin su sayar da kayayyakin su, kuma su sayi abubuwan da ake sarrafawa a Kano. Wannan dalili yasa a cikin karni na sha biyar Sarkin Kano Muhammad Rumfa ya kirkiro kasuwar kurmi domin a dinga yin hada-hadar kasuwanci. Wannan dalili yasa Kano ta bunkasa a harkar kasuwanci.

A takaice dai bunkasar birnin Kano yana alaka da yadda aka samu kyakkyawan shugabanci, da kuma yadda baki suka dinga shigowa daga nahiyoyi daban-daban.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu