TARIHIN SARKIN KANO USMAN MAJE RINGIM

Sarkin Kano Usman wanda ake yiwa lakabi da sunan "Maje Ringim" yayi mulkin Kano daga shekarar 1846 zuwa shekarar 1855, wato dai yayi mulki na tsawon shekara tara. 

Ance farkon abin da Sarkin Kano Usman Maje Ringim ya fara yi a lokacin da ya hau mulki shine ya ginawa mahaifiyar Shekara sa dakin da ba'a taba gina mai girman sa ba a zamanin. Don haka ake kiran mahaifiyar sa da suna "Mai Babban Daki".

Sarkin Kano Usman ya kasance shine babba daga cikin yayan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Ya kasance mutum ne mai halayen kirki, mai hakuri da sanin ya kamata. Wannan saukin halin ne ma yasa baya iya yanke hukunci musamman akan abin da shafi yanke hannu ko kisa. Don haka ne aka ce barayi sun yi yawa a zamanin sa. Haka kuma tarihi ya tabbatar cewa a lokacin sa ba'a samu yaƙe-yaƙe ba, saboda shi ba mai son rigima bane.

Sarkin Kano Usman Maje Ringim ya kasance mutum mai son malamai da kyautata musu. Don haka malamai suka samu dama sosai, har takai sun samu gurbi mai girma a Fadar Masarautar Kano a matsayin masu bada shawara akan Shari'a.

A shekarar 1855 Sarkin Kano Usman Maje Ringim ya tafi Hadeja domin cika umaranin Sarkin Musulmi wanda yace kamo masa Sarkin Hadeja Buhari saboda tawayen da yayi wa Daular Sokoto. A hanyar sa ta zuwa Hadeja ne Allah yayi masa rasuwa a garin Hadeja. Don haka ake kiran sa da suna "Maje Ringim".

Post a Comment

0 Comments

Close Menu